Mai masoya da yawa: Tsaffin 'yan fansho sun sha alwashin yi wa Buhari ruwan kuri'u

Mai masoya da yawa: Tsaffin 'yan fansho sun sha alwashin yi wa Buhari ruwan kuri'u

Tsaffin ma'aikatan kamfanin jiragen saman Najeriya na Nigeria Airways da suka yi ritaya shekaru da dama da suka shude sun bayyana aniyar su ta zubawa Shugaban kasar Najeriya Muhammadu Buhari ruwan kuri'un su a zaben da ke tafe.

Tsaffin ma'aikatan wadanda yanzu haka suke karbar fansho sun bayyana jin dadin su karara ta yandda suka ce gwamnatocin da suka gabata sun yi fatali da bukatun su na biyan hakkokin su tsawon shekaru 14 amma gwamnatin shugaba Buhari ta share masu kukan su.

Mai masoya da yawa: Tsaffin 'yan fansho sun sha alwashin yi wa Buhari ruwan kuri'u

Mai masoya da yawa: Tsaffin 'yan fansho sun sha alwashin yi wa Buhari ruwan kuri'u
Source: Depositphotos

KU KARANTA: Magu ya aikawa Buhari wasikar sirri kan Mai shari'a Onnoghen

Legit.ng Hausa ta samu cewa a cikin wata sanarwa da ma'aikatan suka fitar dauke da sa hannun shugabannin 'yan fanshon na kungiyoyin su Injiniya Lookman Animashaun da kuma Mista Sam Nzene sun ce mambobin su sun shirya gangamin nuna goyon bayan su ga gwamnatin tarayyar.

Mai karatu dai zai iya tuna cewa gwamnatin tarayya karkashin shugabancin Shugaba Muhammadu Buhari ta biya tsaffin ma'aikatan kamfanin jiragen na Nigeria Airways hakkokin su na Fansho da giratuti.

Wannan kamar yadda muka samu ya biyo bayan umurnin da shugaba Muhammadu Buhari ya bayar na biyan su bayan an tantance su.

Kudin dai da aka biya su sun kai sama da Naira biliyan 50 kamar yadda muka samu alkaluma.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma legit.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://web.facebook.com/legitnghausa?_rdc=1&_rdr

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel