Gwamnatin tarayya na kokarin gurgunta gonar Onnoghen - CUPP

Gwamnatin tarayya na kokarin gurgunta gonar Onnoghen - CUPP

- Kungiyar Hadakar jam'iyyun siyasa na Najeriya (CUPP) sun zargi gwamnatin tarayya da shirya makarkashiya ruguza wata gona mallakar Onnoghen

- CUPP din kuma tayi zargin cewa gwamnatin tana cin zarafi ma'aikatan da ke gonar

- Har ila yau, CUPP tayi ikirarin cewa gwamnati tana yiwa lauyoyin da ke kare Onnoghen a kan zargin rashin bayyana kadarorinsa bita da kulli

Kungiyar hadakar jam'iyyun siyasa CUPP ta zargi gwamnatin tarayya da shirya makirci a kan wata gona mallakar Alkalin Alkalai da aka dakatar, Walter Onnoghen a jihar Nasarawa.

Kakakin CUPP, Imo Ugochinyere ne ya yi wannan zargin a wata sanarwa da ya fitar a ranar Talata 5 ga watan Fabrairu kamar yadda The Cable ta ruwaito.

Gwamnatin tarayya na kokarin gurgunta gonar Onnoghen - CUPP

Gwamnatin tarayya na kokarin gurgunta gonar Onnoghen - CUPP
Source: Twitter

DUBA WANNAN: EFCC: Shaida ya bayyana yadda Shekarau da wasu mutane 2 suka kasafta N950m

Kakakin na CUPP ya yi ikirarin cewar wasu mutane da ake zargin makiyaya ne sun yiwa ma'aikatan gonar CJN Onnoghen barazana dake Uke a jihar Nasarawa barazanar cewa su bar wurin ayyukansu.

Ugochinyere ya ce: "Mun samu bayanan sirri daga kwakwarar majiya cewa gwamnati ne ta aika wasu zuwa gonar Onnoghen saboda suna son su toshe dukkan hanyoyin samun kudinsa," inji shi.

"Lauyoyin CJN Onnoghen sun shigar da kara ga hukumomin tsaro inda suka koka kan barazanar da wasu makiyaya suka yiwa ma'aikatan gonar."

Ugochinyere ya kuma ya yi ikirarin cewa gwamnati tana yiwa lauyoyin da ke kare Onnoghen a kan zargin rashin bayyana kadarorinsa a kotun CCT bita da kulli.

Ya ce: "Wasu daga cikin manyan lauyoyin da ke kare CJN Onnoggen sun ce ana gudanar da binciken leken asiri a kansu, ana biye da su duk inda suke zuwa kuma ana sauraron hirar da su keyi a wayoyin tarho dinsu a gida da ofis. Da yawa daga cikinsu sun ce hukumomin tsaro sun fara binciken asusun ajiyarsu."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel