Da duminsa: Mai tsawatarwa a majalisar dokokin jihar Ekiti ta sauya sheka daga PDP zuwa APC

Da duminsa: Mai tsawatarwa a majalisar dokokin jihar Ekiti ta sauya sheka daga PDP zuwa APC

- Mai tsawatarwa a majalisar dokokin jihar Ekiti, Ms Cecilia Dada, ta sauya sheka daga jam'iyyar adawa ta PDP zuwa jam'iyya mai mulki ta APC

- Ta bayyana cewa ta yanke wannan shawarar ne biyo bayan wasu matakai da tsohuwar jam'iyyarta ta dauka, wanda ta ke kallo a matsayin 'kashe jam'iyya'

- APC ta bayyana cewa barakar da PDP ke samu a Ekiti na zama alkairi ga jam'iyyar

Rahotanni sun bayyana cewa mai tsawatarwa a majalisar dokokin jihar Ekiti, Ms Cecilia Dada, ta sauya sheka daga jam'iyyar adawa ta Peoples Democratic Party (PDP) zuwa jam'iyya mai mulki ta All Progressives Congress (APC)

Ms Dada ta bayyana hakan ga manema labarai a ranar Litinin a Ado, babban birnin jihar.

Ta bayyana cewa ta yanke wannan shawarar ne na sauya shekar biyo bayan wasu matakai da tsohuwar jam'iyyarta ta dauka, wanda ta ke kallonsu a matsayin 'kashe jam'iyya'.

Yar majalisar ta kasance ta mambar jam'iyyar PDP ta biyu da ta sauya sheka zuwa APC a cikin makonni biyu.

KARANTA WANNAN: Da yawa sun jikkata a rikicin da ya barke tsakanin masoyan APC da PDP a Delta

Da duminsa: Mai tsawatarwa a majalisar dokokin jihar Ekiti ta sauya sheka daga PDP zuwa APC

Da duminsa: Mai tsawatarwa a majalisar dokokin jihar Ekiti ta sauya sheka daga PDP zuwa APC
Source: Twitter

Kakakin majalisar, Adeniran Alagbada, a makon da ya gabata, ya karbi wani dan majalisa wanda ya sauya sheka zuwa APC, yana mai bayyana cewa barakar da PDP ke samu a Ekiti na zama alkairi ga jam'iyyar APC.

Akwai rabuwar kawuna da sabani a cikin jam'iyyar PDP jihar Ekiti inda ake takun saka tsakanin shugaban marasa rinjaye na majalisar dattijai, Sanata Abiodun olujimi, da kuma tsohon gwamnan jihar, Me Ayodele Fayose, wadanda ke jagorantar bangarori daban daban na jam'iyyar wanda kuma ya kawo rabuwar kawunan mambobin jam'iyyar.

Tsohon gwamnan jihar, Fayose ya dauki rikicin zuwa mataki na gaba a lokacin da ya shiga wani gidan rediyo ya bukaci al'ummar jihar da kar su zabi Sanata Olujimi wanda shi ne dan takarar sanatan mazabar Ekiti ta Kudu a karkashin jam'iyyar PDP.

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel