Ambaton sunan PDP yana saka min ciwon kai - Farfesa Osinbajo

Ambaton sunan PDP yana saka min ciwon kai - Farfesa Osinbajo

Mataimakin shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo ya ce ambaton sunan jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP) na janyo masa ciwon kai.

Osinbajo ya yi wannnan furucin ne a taron kaddamar da yakin neman zaben shugaban kasa da akayi a Akure da ke jihar Ondo a ranar Talata.

Duk da cewa bai ambaci sunan PDP karara ba, kowa ya fahimci cewa yana magana ne a kan jam'iyyar PDP da ta mulki kasar na tsawon shekaru 16.

Ya zargi jam'iyyar PDP ta rashin kulawa da jin dadin 'yan Najeriya na tsawon shekaru 16 da tayi mulki a kasar.

Ambaton PDP yana saka min ciwon kai - Farfesa Osinbajo

Ambaton PDP yana saka min ciwon kai - Farfesa Osinbajo
Source: Twitter

DUBA WANNAN: EFCC: Shaida ya bayyana yadda Shekarau da wasu mutane 2 suka kasafta N950m

"Kada mu rudi kanmu. Abinda ke kawo mana koma baya shine rashawa. Wannan shine dalilin da yasa ba zamu koma baya ba; dukkana abubuwan da muke aikatawa yanzu ya kamata da anyi su a baya," inji shi.

"Ya dace yanzu mun kammala titin Legas zuwa Ibadan. Amma yanzu muka fara saboda wadanda suka ce za suyi karya su kayi, ba zan ambaci sunansu ba. Ba mu son fadin sunansu domin ciwon kai yake janyo mana.

"Sun ce sun fara aikin titin Legas zuwa Ibadan amma duk karya ne. Kowanne kasafin kudi karya su ke yi. Yanzu muke aikin. Gwamnatin Muhammadu Buhari ne ta fara aikin kuma zamu kammala. Idan ka bi hanyar zaka ga aikin da ake yi."

Mataimakin shugaban kasar ya ce gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari tana ciyar da yara miliyan 9.2 a jihohi 26 a kullum a karkashin shirin ciyar da daliban makaranta.

Ya ce ana amfani da kwai miliyan 6.8 a duk mako kuma hakan yana samar da ayyukan yi ga manoma.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel