Karshen zance: Magu da shugaban kasa sun tattauna makomar korarren Alkalin-alkalai

Karshen zance: Magu da shugaban kasa sun tattauna makomar korarren Alkalin-alkalai

Shugaban rikon kwarya na hukumar gwamnatin tarayya dake yaki da masu yiwa tattalin arzikin kasa zagon kasa watau Economic and Financial Crimes Commission (EFCC), Ibrahim Magu mun samu labarin cewa ya rubutwa shugaba Muhammadu Buhari takarda game da Mai shari'a Walter Onnoghen.

Kamar yadda muka samu, takardar wadda shugaban na EFCC ya rubutawa Shugaba Buhari a karshen watan da ya gabata wacce ta sirri ce wasu 'yan jaridu sun same ta ne ranar Talata da ta gabata ta hannun wata kungiya mai zaman kan ta ta Coalition of United Political Parties (CUPP).

Karshen zance: Magu da shugaban kasa sun tattauna makomar korarren Alkalin-alkalai

Karshen zance: Magu da shugaban kasa sun tattauna makomar korarren Alkalin-alkalai
Source: Depositphotos

KU KARANTA: An kama wani ustazu da kan mutum a jihar Ogun

Legit.ng Hausa ta samu a cikin takardar wacce ta sirri ce cewar yana mai shaidawa shugaban kasar cewa tuni suka soma bincike kan harkallar kuma har ma sun fitar da rahoton wucin gadi kan lamarin.

Haka zalika a cikin rahoton, Mista Magu ya shaidawa Shugaba Buhari cewa a dan binciken da suka fara sun gano Alkalin-alkalan yana da makudan kudaden da suka wuce mizanin samun sa na gida da na waje a asusun ajiya na bankuna da dama.

Mista Magu ya cigaba da cewa hukumar ta su ta jinkirta ne da binciken sa sakamakon mukamin da yake rike da shi a baya amma da tuni sun ida binciko dukkan abinda ake tuhumar sa da shi amma yanzu tuni jami'an sa suka dukufa domin kai karshen binciken.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma legit.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://web.facebook.com/legitnghausa?_rdc=1&_rdr

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel