Allah-kare-bala'i: Dakin kwanan dalibai ya kama da wuta a jami'ar jihar Kano

Allah-kare-bala'i: Dakin kwanan dalibai ya kama da wuta a jami'ar jihar Kano

Wutar dare ta kona dakunan kwana na Dangote da ya ginawa dalibai mata a jami'ar kimmiyya da fasaha ta jihar Kano dake da masauki a garin Wudil kamar dai yadda muka samu daga majiyoyin mu.

Gobarar dai kamar yadda muka samu, an alakan ta ta ne da matsalar wutar lantarki da ta auku kamar dai yadda wata sanarwar manema labarai da jami'in hulda da jama'a na jami'ar Malam Abdullahi Datti Abdullahi ya fitar dauke da sa hannun sa.

Allah-kare-bara'i: Dakin kwanan dalibai ya kama da wuta a jami'ar jihar Kano

Allah-kare-bara'i: Dakin kwanan dalibai ya kama da wuta a jami'ar jihar Kano
Source: Twitter

KU KARANTA: Wata mai ciki ta damfari Dangote

Legit.ng Hausa ta samu cewa kamar dai yadda hukumar jami'ar ta bayyana, gobarar ta soma tashi ne da karfe 9:30 na daren ranar Talatar din da ta gabata.

Sai dai sanarwar kuma ta cigaba da cewa tashin gobarar ke da wuya sai mahukuntan makarantar suka sanar da jami'an hukumar kashe gobara ta gwamnatin tarayya, shiyyar jihar Kano da sauran hukumomi da ma'aikatun dake makwaftaka da su wadanda suka kai masu dauki.

Sanarwar ta kara da cewa ba'a samu rasawa ko kuma jikkatar rayuwaka ko daya ba sakamakon yakin aikin da akeyi na kungiyar malaman jami'o'in kasa watau Academic Staff Union of Universities (ASUU) dukkan daliban ba su nan.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma legit.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://web.facebook.com/legitnghausa?_rdc=1&_rdr

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel