Atiku Abubakar ya lakanci tattalin arzikin Najeriya – Peter Obi

Atiku Abubakar ya lakanci tattalin arzikin Najeriya – Peter Obi

- Jirgin yakin neman zaben PDP na Peter Obi ya shiga wata kasuwa a Legas

- Abokin takarar Atiku watau P. Obi yace PDP za ta habaka tattalin Najeriya

- ‘Dan takarar Mataimakin Shugaban kasar yace shi da Atiku sun san tattali

Atiku Abubakar ya lakanci tattalin arzikin Najeriya – Peter Obi

Peter Obi yace Atiku zai magance matsalolin Najeriya
Source: Twitter

‘Dan takarar mataimakin shugaban kasa na babbar jam’iyyar adawa ta PDP a zaben bana na 2019, Peter Obi, ya bayyana cewa jam’iyyar su ce za ta iya shawo kan irin manyan matsalolin da su kayi wa Najeriya katutu a halin yanzu.

Peter Obi yayi wannan bayani ne a wata babbar kasuwa da ake kira Alaba International Market da ke cikin Ojo a Garin Legas. ‘Dan takarar yace za su kawo karshen rashin aikin yi da duk wata matsalar tattalin arziki a kasar.

KU KARANTA: Atiku yayi alkawarin dakatar da yajin aiki a Jami’o’i a ranar farko a ofis

Mista Peter Obi yake cewa Atiku Abubakar, ya san harkar tattalin arziki saboda aiki da yayi a matsayin mataimakin shugaban kasar nan, don haka zai iya gyara tattalin Najeriya idan har ya samu zama shugaban kasa a zaben bana.

A cewar ‘dan takarar mataimakin shugaban kasar na PDP, Atiku ya rike mukami a Najeriya kuma an ga irin kwarewar sa, sannan kuma hamshakin ‘dan kasuwa ne wanda yayi zarra a fannonin da ya shiga, don haka ya nemi a zabe sa.

Obi yake cewa shi karan kan-sa yayi gwamna a jihar Anambra, kuma bayan nan yana taba kasuwanci don haka yake ganin ilmin sa da kwarewar sa za su yi amfani wajen kawo karshen rashin aikin yi a kasar nan idan su ka samu mulki.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel