Jerin sunaye: Gwamnatin tarayya ta bayar da lasisi ga sabbin jami’o’I 4

Jerin sunaye: Gwamnatin tarayya ta bayar da lasisi ga sabbin jami’o’I 4

Gwamnatin tarayya ta bayar da lasisin ga wasu sabbin jami’o’i ma su zaman kan su guda 4, lamarin da ya jawo karuwar adadin jami’o’i ma su zaman kan su da ke ksar nan ya zuwa 79.

Sabbin jami’o’in da aka bawa lasisin su ne; Jami’ar Greenfield da ke Kaduna, Jami’ar Dominion da ke Ibadan, Jami’ar Trinity da ke jihar Ogun, da kuma jami’ar Westland da ke jihar Osun.

Da ya ke jawabi a wurin taron bayar da lasisin, ministan ilimi, Malam Adamu Adamu, ya ce za a cigaba da sa ido a kan harkokin sabbin jami’o’in har na tsawon shekara uku kafin daga bisani a hada su da tsofin jami’o’I da za su cigaba da kula da al’amuran su.

Ministan da shugaban hukumar JAMB, Farfesa Ishaq Oloyede, ya wakilta y ace jami’o’i 164 ne ke bayar da ilimi ga ‘yan Najeriya miliyan 200.

Jerin sunaye: Gwamnatin tarayya ta bayar da lasisi ga sabbin jami’o’I 4

Adamu Adamu; Ministan Ilimi
Source: UGC

A nasa bangaren, sakataren hukumar kula da jami’o’i na kasa (NUC), Farfesa Abubakar Rasheed, ya ce an samu tsawon shekaru 16 ana sa ido da lura da harkokin jami’o’in kafin a basu lasisin cin gashin kan su.

A ranar Litinin din wannan makon ne Legit.ng ta kawo ma ku labarin cewar gwamnatin tarayya ta bayyana cewar za ta rushe haramtattun makarantun gaba da sakandire saboda irin barazanar da su ke yi ga tsarin ilimi a kasar nan.

DUBA WANNAN: Zagon kasa: Tambuwal ya salami daya daga cikin kwamishinonin sa

Tuni gwamnatin tarayya ta bawa hukumar kula da makarantun gaba da sakandire umarnin daukan matakan gaggawa a kan haramtattun jami'o'i, kwalejin kimiyya, da kwalejin horon malamai da ke fadin kasar nan.

Yanzu haka gwamnatin tarayya ta yi nasarar gano haramtattun jami'o'i 66 da kwalejin kimiyya 68 da ke aiki tare da bayar da takardun shaidar kammala karatu ga jama'a.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel