ASUU: Ina zama Shugaban kasa, 'Dalibai za su koma karatu inji Atiku

ASUU: Ina zama Shugaban kasa, 'Dalibai za su koma karatu inji Atiku

Mun ji cewa babban ‘dan takarar jam’iyyar hamayya a Najeriya watau Atiku Abubakar na PDP, ya bayyana cewa zai kawo karshen yajin aikin da ake yi a jami’o’in gwamnati da zarar ya zama shugaban kasa.

ASUU: Ina zama Shugaban kasa, 'Dalibai za su koma karatu inji Atiku

Ranar da na zama Shugaban kasa zan zauna da ASUU - Atiku
Source: Depositphotos

Kamar yadda mu ka samu labari, ‘dan takarar na PDP ya bayyana wannan ne a wajen wani biki da kamfanin Silverbird ta shirya a Garin Legas a Ranar Lahadin da ta gabata. Atiku yace yajin aikin yana hana karatu tafiya a kasar.

Alhaji Atiku Abubakar ya koka da yadda yajin aikin malaman makarantar wanda wani lokaci a kan shafe tsawon fiye da watanni 4 ana fama ke kawowa dalibai cikas a Najeriya. Atiku yayi alkawarin zai gyara wannan lamari.

KU KARANTA: Hotunan irin tarbar da aka yi wa Shugaba Buhari a Jihar Ekiti

‘Dan tajarar shugaban kasar ya sha alwashin sauraron bukatun malaman jami’o’in kasar idan ya samu mulki a zaben da za ayi kwanan nan. Atiku yace wannan ne abin da zai fara tun a ranar farko da ya shiga ofishin shugaban kasa.

Atiku Abubakar ya nuna bacin ran sa ga halin da ake ciki yanzu a Najeriya inda aka yi kusan kwanaki 90, malaman jami’o’i na yajin aiki. Atiku yace da zarar ya samu nasarar zama shugaban kasa, za a bude makarantun Najeriya.

Babban Abokin gaban na shugaba Buhari dai yayi alkawarin nada mukarraban sa tare da kuma kokarin ganin ‘daliban Jami’a sun koma karatu yayin da ya soma shiga ofis. ‘Dan takarar ya kuma yi alkawarin sa kudi a harkar ilmi.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel