Zabe: Wata babbar kungiya a arewa ta musanta mara wa Atiku baya

Zabe: Wata babbar kungiya a arewa ta musanta mara wa Atiku baya

Wani tsagi na kungiyar ‘yan arewa ta tsakiya sun musanta bayyana goyon baya ga dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar PDP, Alhaji Atiku Abubakar.

A wani jawabi da sakataren yada labarai na kungiyar, Mista Gowon Egbunu, ya fitar a jiya, Talata, a Abuja, kungiyar ta ce ba ta taba zama tare da amince wa da goyon bayan Atiku a matsayin dan takarar ta na shugaban kasa ba a zabe mai zuwa.

A ranar Lahadi ne rahotanni su ka bayyana cewar kungiyar ‘yan arewa ta tsakiya sun bi sahun wasu kungiyoyi da dama wajen bayyana goyon baya ga takarar Atiku Abubakar.

Ragowar kungiyoyin da rahotannin su k ace sun bayyana goyon baya ga takarar Atiku bayan kamala wani taro a Abuja, sun hada da kungiyar Ohanaeze Ndigbo, Kungiyar yankin Neja-Delta da kuma wani tsagi na kungiyar Afenifere.

Zabe: Wata babbar kungiya a arewa ta musanta mara wa Atiku baya

Atiku
Source: UGC

Sai dai a cikin jawabin sakataren yada labaran kungiyar ‘yan arewa ta tsakiya, Egbunu y ace Atiku bad an takarar su ba ne kuma ba zai taba zama zabin su ba.

A daya bangaren, tsofin janar a rundunar soji ta sama, kasa, da ruwa sun bayyana goyon bayan su ga takarar shugaba Buhari domin sake zama shugaban kasar Najeriya a karo na biyu.

DUBA WANNAN: Kowa ya yi zagi a kasuwa: Ba zan nemi nemi tazarce fiye da sau 2 ba – Buhari

A ranar Litinin ne tsofin janar din sojin su ka shaida wa duniya goyon bayan su ga takarar shugaba Buhari a zaben da za a yi ranar 16 ga watan Fabarairu da mu ke ciki.

Tsofin janara-janar din sun hada da ma su mukamin manjo janar 13, Air Vice Marshal (AVM) 8, Rear Admiral 2, birgediya janar 12, Air Commodore 9, Commodore 8 da kuma wasu tsofin shugabannin rundunar soji 17.

Tsohon gwamnan jihar Legas a mulkin soji, Birgeiya janar Buba Marwa (mai ritaya) ne ya jagoranci tsofin janar-janar din yayin da su ka ziyarci shugaba Buhari a fadar sa ta mulki domin bayyana goyon bayan su ga takarar sa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel