Zaben 2019: Zakzaky ya umurci mabiyan sa kar su zabi Buhari da Atiku a zabe mai zuwa

Zaben 2019: Zakzaky ya umurci mabiyan sa kar su zabi Buhari da Atiku a zabe mai zuwa

Maganganu sun yi ta yawo kan yiyuwar shigan 'yan Shi'a babban zabe me zuwa a kasar nan da za'a fara ranar 16 ga watan biyu musamman ganin yadda a baya sukan kauracewa shiga harkokin zaben ciki kuwa hadda takara da jefa kuri'a.

Haka a 'yan kwanakin nan wasu rohatanni sun bayyana cewa almajiran na Zakzaky da ke da yawa a wasu daga jahohin arewacin kasar nan zasu bada dukkan kuri'unsu ga Alhaji Atiku Abubakar dan takarar shugaban kasar Najeriya a karkashin Jam'iyar Adawa ta PDP.

Zaben 2019: Zakzaky ya umurci mabiyan sa kar su zabi Buhari da Atiku a zabe mai zuwa

Zaben 2019: Zakzaky ya umurci mabiyan sa kar su zabi Buhari da Atiku a zabe mai zuwa
Source: Twitter

KU KARANTA: Wata mata mai ciki ta damfari Dangote

Legit.ng Hausa ta samu cewa sai dai a ranar Asabar 26/01/2019, wasu daga makusantan Shaik Ibraheem Zakzaky sun ziyarce shi a wajan da ake tsare da shi sannan ya yi magana kan zantukan da ake yadawa kansu akan zaben inda suka ce yace su kauracewa zaben da za'a yi.

Wasu daga wadanda suka ziyarci Zakzaky din sun ambato shi yana cewa “To mu muna zabe ne? Ina ruwan mu da zaben su. Kuma ma mu ai ba'a sanmu da hargitsi ba, idan ma haka ne. Su kansu wannan al'ummar sun yi mana shaida akan cewa mu ba masu hargisti bane” inji shi.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma legit.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://web.facebook.com/legitnghausa?_rdc=1&_rdr

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel