Dankari: Akalla karuwai 10,000 sun dira Abuja domin nuna goyon bayansu ga Atiku Abubakar

Dankari: Akalla karuwai 10,000 sun dira Abuja domin nuna goyon bayansu ga Atiku Abubakar

Akalla yan gidan magajiya dubu goma karkashin kungiyar karuwai ta Najeriya, NANP sun dira babbar birnin tarayya Abuja ranan Talata gabanin zaben shugaban kasa da yan majalisa da zai gudana ranan 16 ga watan Febrairu, 2019.

Kungiyar ta sammaci sukkan mambobinta daga fadin tarayya domin dan takaran shugaban kasa karkashin Peoples Democratic Party, PDP, Alhaji Atiku Abubakar.

Tabbatar da labarin, sakatariyar kungiyar, Sandra Efosa, ta bayyana cewa sun zabi Alhaji Atiku Abubakar ne bayan kyakkyawan lura da manufofinsa na tsawon makonni da yawa.

Efos ta kara da cewa karkashin wannan gwamnati, basu samun isasshen kudi sakamakon matsin tattalin arziki.

Tace: "Yanzu na shigo Abuja da shugabarmu, Tamar Tion da mambobi 10,000 gabanin zaben shugaban kasa domin marawa Alhaji Atiku Abubakar baya."

"Za muyi kira ga mambobinmu a fadin tarayya domin aiki ga dan takaran PDP. Zan sanar da kai matakin da zamu dauka nan gaba."

Legit Hausa ta kawo muku rahoton cewa wata kungiyar mayu ta marawa Atiku Abubakar dan takarar Shugaban kasa a jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) baya a matsayin zabinsu a zaben 2019 mai zuwa.

Wannan kungiyar mai suna Association of White Witches in Nigeria (AWWN) sun nuna goyon bayansu ga dan takarar Shugaban kasa na PDP bayan tattaunawa daban-daban wanda suka yi ikirarin sunyi a dutsen Obudu da na Zuma.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit Newspaper

Tags:
Mailfire view pixel