Kowa ya yi zagi a kasuwa: Ba zan nemi nemi tazarce fiye da sau 2 ba – Buhari

Kowa ya yi zagi a kasuwa: Ba zan nemi nemi tazarce fiye da sau 2 ba – Buhari

A wani salon a gugar zana ga tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ce ba zai nemi tazarce a karo na uku ba kamar yadda wasu su ka so yi ba a baya.

Da ya ke jawabi ga taron sarakunan gargajiya a jihar Ondo, Buhari ya ce, “mun kamala zango na daya kuma mu na neman na biyu. Bayan zagaye na biyu, kundin tsarin mulkin Najeriya bai amince da sake neman mulki ba.”

Ya kara da cewa, “akwai wadanda su ka yi kokarin ganin sun karya tsarin kundin mulkin Najeriya amma ba su yi nasara ba. Mun koyi darasi daga kuskuren da su ka aikata.

Mai watsa labaran shugaba Buhari a dandalin sada zumunta, Tolu Ogunlesi, ne ya wallafa wadannan kalamai na Buhari a shafin san a Tuwita.

Kowa ya yi zagi a kasuwa: Ba zan nemi nemi tazarce fiye da sau 2 ba – Buhari

Buhari da Osinabjo a jihar Ekiti
Source: Twitter

A karshen zangon mulkin Obasanjo na biyu ne aka samu barkewar cece-kuce a kasa a kan zargin tsohon shugaban kasar da yunkurin cigaba da rike madafun iko a karo na uku. Wannan kudiri na Obasanjo ta haifar da mahawara mai zafin gaske a tsakanin 'yan majalisar tarayya.

DUBA WANNAN: Cin hanci: Har yanzu akwai hukumomin gwamnati da ke karkatar da kudin shuga - Buhari

An zargi Obasanjo da bayar da cin hancin makudan kudi ga 'yan majalisun wakilai da na majalisar dattijai domin su sahale ma sa ya cigaba da mulkin Najeriya bayan kammala zango na biyu a mulki.

Sai dai duk da makudan kudin da ake zargin Obasanjo da bawa 'yan majalisar da wasu manyan 'yan siyasar Najeriya da sarakuna, burin sa bai samu cika ba.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel