Kotu ta yanke wa wani mutun shekara 10 a gidan yari kan kashe abokinsa saboda musun wanda ya lashe zaben 2015

Kotu ta yanke wa wani mutun shekara 10 a gidan yari kan kashe abokinsa saboda musun wanda ya lashe zaben 2015

- Wata babbar kotun Lagas da ke zama a Igbosereta yankewa wani Kamoru Kushimo shekaru 10 a gidan yari

- An tuhume shi da laifin soke abokinsa da wuka har lahira a lokaci wani musu kan wanda zai yi nasarar lashe zaben kasar na 2015

- Wanda ake karan bai amsa laifinsa ba amma aka tsare shi a kurkuku

Wata babbar kotun Lagas da ke zama a Igbosere a ranar Talata ta yankewa wani Kamoru Kushimo shekaru 10 a gidan yari kan laifin soke abokinsa da wuka har lahira a lokaci wani musu kan wanda zai yi nasarar lashe zaben kasar na 2015.

Ma’aikatar tsaro na jihar Lagas ta gurfanar da Kushimo a ranar 10 ga watan Fabrairun 2016 inda ta tuhume shi da yanka mutum.

Kotu ta yanke wa wani mutun shekara 10 a gidan yari kan kashe abokinsa saboda musun wanda ya lashe zaben 2015

Kotu ta yanke wa wani mutun shekara 10 a gidan yari kan kashe abokinsa saboda musun wanda ya lashe zaben 2015
Source: Twitter

Wanda ake karan bai amsa laifinsa ba amma aka tsare shi a kurkuku.

Justis Sedoten Ogunsanya ta yankewa Kushimo hukunci bayan sake duba hujjoin da aka gabatar kan shari’an.

KU KARANTA KUMA: PDP ta dage kamfen dinta saboda kisan yar’uwar sanata da wasu da yan fashi suka yi a Zamfara

Ogunsanya tace an kama wanda ake karan da laifin yanka mutum don haka ta yanke masa hukuncin da ya dace.

Mai shari’an ta bayyana cewa duba ga hujjojin da aka gabatar a gabanta, lauyan gwamnati ya tabbatar da hujjojin nasa yadda ya kamata.

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel