2019: Jami’an tsaro na neman mu da sharri a Najeriya - Kungiyar IMN

2019: Jami’an tsaro na neman mu da sharri a Najeriya - Kungiyar IMN

Mun ji labari cewa kungiyar nan wanda tayi fice a Najeriya ta The Islamic Movement ta Mabiya addinin Shi’a sun bayyana cewa shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kusa barin karagar mulkin kasar.

2019: Jami’an tsaro na neman mu da sharri a Najeriya - Kungiyar IMN

Mabiya IMN sun ce Shugaba Buhari zai fadi zaben 2019
Source: Depositphotos

Kungiyar da aka fi sani da IMN tace shugaba Buhari zai sha kasa ne a zaben na 2019 da za ayi kwanan nan. Babban kungiyar addinin ta ce shugaban kasar tuni ya fara hango rashin nasara don haka yake kokarin hana ayi zabe a Najeriya.

Kakakin kungiyar na Najeriya mai suna Ibrahim Musa shi ya bayyanawa ‘yan jarida wannan a jiya Litinin. Musa yace gwamnatin Najeriya na kokarin kitsa rikici na babu gaira babu dalili domin a nemi a dakatar da zaben da aka shirya.

IMN tayi ikirarin cewa hukumar tsaro na DSS ta aikawa manyan jami’an tsaro na Najeriya wata takarda a boye inda aka nemi a ga bayan ‘ya ‘yan kungiyar na Shi’a. Ibrahim Musa yace wannan wasika da aka aika ta shigo har hannun su.

KU KARANTA: An kama sojan da aka kora daga aiki a cikin gungun ‘yan fashi

Mai magana da yawun bakin kungiyar ta Shi’a yace DSS din na zargin IMN da neman shirya zanga-zanga wanda ka iya kai wa ga rikici a manyan Garuruwan Arewa irin su Kano, Kaduna, Sokoto da kuma babban birnin tarayya Abuja.

Musa wanda yake magana a madadin kungiyar ta IMN yace babu gaskiya a wannan kishin-kishin din da yake yawo a wajen jami’an tsaron kasar. Sai dai kungiyar tace ana kokarin yin rufa-rufa ne na kisan gillar da aka yi mata kwanakin baya.

Tun 2015 dai ake fama da ‘yan shi’a a Najeriya inda har ta kai a kama babban jagoran na kungiyar IMN Ibrahim Zakzaky wanda har gobe yake tsare. Kungiyar tana nema gwamnatin kasar ta saki malamin na ta.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Legit

Online view pixel