Yanzu-yanzu: Kakakin gwamnatin Aminu Tambuwal ya fita daga PDP zuwa APC

Yanzu-yanzu: Kakakin gwamnatin Aminu Tambuwal ya fita daga PDP zuwa APC

Kwamishanan labaran jihar Sokoto, Barista Bello Muhammad Goronyo, ya sauya sheka daga jam'iyyar Peopes Demcratic Party PDP zuwa All Progressives Congress (APC).

Goronyo ya kasance mai magana da yawun gwamnatin jihar kuma kakakin yakin neman zaben gwamna Aminu Waziri Tambuwal a zaben da zai gudana a makonni masu zuwa.

Ya sanar da sauya shekarsa ne ranan Talata a taron kaddamar da yakin neman zaben APC da akayi a garin Wammako, mahaifar jigon jam'iyyar APC na jihar, Sanata Aliyu Magatakarda Wammako.

Wannan babban karuwa da APc ta samu ya farantawa mabiyan jam'iyyar ciki sosai. Amma Goronyo bai bayyana dalilansa na fita daga gwamnatin Tambuwal ba.

Wata majiya a PDP ta bayyana cewa ana kyautata zaton cewa kwamishanan ya sauya sheka ne saboda rashin samun tikitin takarar kujeran dan majalisan tarayya mai wakilta Goronyo/Gada.

Majiyar ta kara da cewa saboda haka yasa gwamna Aminu Waziri Tambuwal ya bashi kwamishanan labarai bayan faduwarsa a zaben fidda gwanin.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel