Yan bindiga sun kashe mutum 15 sun sace mata 6 a Zamfara

Yan bindiga sun kashe mutum 15 sun sace mata 6 a Zamfara

- Yan sandan Zamfara sun tabbatar da cewa yan bindiga sun kashe mutum 15

- Yan bindiga sun kai hari kauyukan Wonaka, Ajja, Mada, Ruwan Baure, Doka, Takoka da kuma Tudun-Maijatau da ke yankin Mada a Gusau

- Maharan sun kuma yi garkuwa da mata shida da wani namiji daya

Rundunar yan sanda a Zamfara sun tabbatar da cewa yan bindiga sun kashe mutum 15 da sace mata shida a karamar hukumar Gusau da ke jihar.

Jami’in hulda da jama’a na rundunar, SP Muhammad Shehu, ya tabbatar da akan a wani jawabi a Gusau.

Shehu ya bayyana cewa a ranar Litinin, an kai hari kauyukan Wonaka, Ajja, Mada, Ruwan Baure, Doka, Takoka da kuma Tudun-Maijatau da ke yankin Mada a Gusau.

Yace wata mace na cikin wadanda aka kashe, inda ya kara da cewa maharan sun kuma yi garkuwa da mata shida da wani namiji daya.

Yan bindiga sun kashe mutum 15 sun sace mata 6 a Zamfara

Yan bindiga sun kashe mutum 15 sun sace mata 6 a Zamfara
Source: Depositphotos

Sai dai ya bayyana cewa abubuwa sun lafa inda jama’a suka kama harkokin gabansu a yankin.

A baya mun ji cewa jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) ta dakatar da kamfen dinta na neman takarar gwamna a jihar Zamfara biyo bayan sabbin hare-hare da yan fashi suka ki garuruwa a jihar.

KU KARANTA KUMA: APC ta yi mana rashin adalci a Zamfara - Inji Gwamna Yari

Dan takarar gwamna na jam’iyyar, Alhaji Bello Matawalle ya sanar da wannan hukunci a wani taron manema labarai a Gusau a ranar Talata, 5 ga watan Fabrairu.

Matawalle wanda ya nuna damuwa kan hare-haren, ya yi korafin cewa lamarin ya fara daukar wani hanya na daban.

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel