Cikin Hotuna: Shugaba Buhari yayin rantsar da sabon shugaban hukumar ICPC

Cikin Hotuna: Shugaba Buhari yayin rantsar da sabon shugaban hukumar ICPC

A ranar Litinin din da ta gabata ne jaridar Legit.ng ta ruwaito cewa, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya rantsar da sabon shugaban hukumar yaki da rashawa mai zaman kanta ta ICPC, Independent Corrupt Practices Commission.

Bayan tsawon kimanin watanni bakwai da mika sunan sa domin neman amincewa majalisar dokoki ta tarayyar kasar nan, shugaban kasa Buhari a jiya Litinin ya rantsar da Farfesa Bolaji Owasanoye a matsayin sabon shugaban hukumar ICPC.

Shugaba Buhari yayin rantsar da sabon shugaban hukumar ICPC

Shugaba Buhari yayin rantsar da sabon shugaban hukumar ICPC
Source: Twitter

Majalisar zantarwa yayin rantsar da sabbin mambobin hukumar ICPC

Majalisar zantarwa yayin rantsar da sabbin mambobin hukumar ICPC
Source: Twitter

Shugaba Buhari yayin rantsar da sabbin mambobi da shugaban hukumar ICPC

Shugaba Buhari yayin rantsar da sabbin mambobi da shugaban hukumar ICPC
Source: Twitter

Sabbin mambobi yayin karbar rantsuwa a fadar Villa

Sabbin mambobi yayin karbar rantsuwa a fadar Villa
Source: Twitter

Jerin sabbin mambobin hukumar ICPC da shugaba Buhari ya rantsar

Jerin sabbin mambobin hukumar ICPC da shugaba Buhari ya rantsar
Source: Twitter

Shugaba Buhari yayin rantsar da daya daga cikin mambobin hukumar ICPC

Shugaba Buhari yayin rantsar da daya daga cikin mambobin hukumar ICPC
Source: Twitter

Shugaba Buhari yayin rantsar da sabbin mambobi da shugaban hukumar ICPC

Shugaba Buhari yayin rantsar da sabbin mambobi da shugaban hukumar ICPC
Source: Twitter

Sabbin mambobin hukumar ICPC yayin karbar rantsuwa

Sabbin mambobin hukumar ICPC yayin karbar rantsuwa
Source: Twitter

Kamar yadda kafofin watsa labarai na Sahara Reporters da kuma Channels TV suka ruwaito, taron bikin rantsuwar ya gudana ne a babban dakin taro na Council Chamber da ke fadar shugaban kasa ta Villa cikin babban birnin kasar nan na tarayya.

Kazalika shugaba Buhari ya rantsar da wasu jiga-jigan mambobi na hukumar ta ICPC da suka hadar da Hajiya Hannatu Muhammad 'yar asalin jihar Jigawa mai shekaru 27 kacal a duniya bisa ga tanadin hukumar na sanya Matashi a cikin jagororin ta.

KARANTA KUMA: Zargi: Hadimin Buhari ya bayyana tuggun da Atiku ya kulla idan yayi nasara a zaben 2019

Sauran mambobin sun hadar da; Grace Chinda daga jihar Delta, Olubukola Balogun daga jihar Legas, Okola Titus na jihar Enugu, Obiora Iqwedebia daga jihar Anambra, Adamu Bello daga jihar Katsina, Abdullahi Maikanu Saidu na jihar Neja, da kuma Yahaya Umah Dauda na jihar Nasarawa.

Cikin jawaban su da sanadin sabon shugaban hukumar, Farfesa Owasonaye ya ce ba za su bai wa kasar nan kunya ba. Kazalika shugaba Buhari ya ce gwamnatin sa ba za ta gaza wajen ci gaba da zage dantse da fafatawa wajen yaki da rashawa a kasar nan.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na zaurukan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel