PDP ta dage kamfen dinta saboda kisan yar’uwar sanata da wasu da yan fashi suka yi a Zamfara

PDP ta dage kamfen dinta saboda kisan yar’uwar sanata da wasu da yan fashi suka yi a Zamfara

- Jam'iyyar PDP ta dakatar da kamfen dinta na neman takarar gwamna a jihar Zamfara biyo bayan sabbin hare-hare da yan fashi suka ki garuruwa a jihar

- Alhaji Bello Matawalle dan takarar gwamna na jam'iyyar ya sanar da wannan hukunci a wani taron manema labarai

- Ya yi kira ga gwamnati da hukumomin tsaro da su dauki mataki da zai kawo karshen ayyukan yan fashi

Jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) ta dakatar da kamfen dinta na neman takarar gwamna a jihar Zamfara biyo bayan sabbin hare-hare da yan fashi suka ki garuruwa a jihar.

Dan takarar gwamna na jam’iyyar, Alhaji Bello Matawalle ya sanar da wannan hukunci a wani taron manema labarai a Gusau a ranar Talata, 5 ga watan Fabrairu.

PDP ta dage kamfen dinta saboda kisan yar’uwar sanata da wasu da yan fashi suka yi a Zamfara

PDP ta dage kamfen dinta saboda kisan yar’uwar sanata da wasu da yan fashi suka yi a Zamfara
Source: Depositphotos

“Ina son sanar da cewa na dakatar da dukkanin shirye-shiryen kamfen dina saboda yawan hare-haren da yan fashi ke ci gaba da kaiwa jihar.

“Ina kuma so na yi kira ga gwamnati da hukumomin tsaro da su dauki mataki da zai kawo karshen ayyukan yan fashi,” inji shi.

Matawalle wanda ya nuna damuwa kan hare-haren, ya yi korafin cewa lamarin ya fara daukar wani hanya na daban.

KU KARANTA KUMA: APC ta yi mana rashin adalci a Zamfara - Inji Gwamna Yari

A baya Legit.ng ta rahoto cewa wasu yan fashi da makami sun kashe Ade Marafa, babbar yayar Kabir Marafa, Sanata mai wakiltan Zamfara ta tsakiya, sannan suka sace mijinta.

Abubakar Tsafe, wani hadimin sanatan wanda ya tabbatar da lamarin yace yan fashin sun kai farmaki gidan yayar sanatan da ke Ruwan Bore na karamar hukumar Gusau a ranar Talata, 5 ga watan Fabrairu.

Hadimin ya bayyana cewa yan fashin da yawansu ya kai 100 sun sanya ma kauyen wuta bayan harin.

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel