Yaki da cin hanci da rashawa ba abune mai sauki ba ko kadan - Buhari

Yaki da cin hanci da rashawa ba abune mai sauki ba ko kadan - Buhari

- Shugaban kasa Muhamadu Buhari ya tabbatar da cewa yaki da cin hanci da rashawa a kasa kamar Najeriya ba abu ne mai sauki ba ko kadan

- Buhari yace duk da babban aikin da ke tattare da hakan, ba zai taba gajiyawa ba wajen fitar da kasar daga kangin da take ciki ba kamar yadda yayi alkawarin kawo karshen cin hanci da rashawa a kasar a 2015

- Mataimakin Shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo ya soki yadda PDP tayi ta kashe-kashen kudi a shekaru 16 da tayi tana mulki

Shugaban kasa Muhamadu Buhari a ranar Talata, 5 ga watan Fabrairu ya tabbatar da cewa yaki da cin hanci da rashawa a kasa kamar Najeriya ba abu ne mai sauki ba ko kadan.

Ya bayyana hakan ne yayinda yake jawabi ga taron magoya bayan ja’iyyar APC a Ekiti Parapo da ke Ado Ekiti a lokacin gangamin kamfen dinsa a jihar Ekiti.

Yaki da cin hanci da rashawa ba abune mai sauki ba ko kadan - Buhari

Yaki da cin hanci da rashawa ba abune mai sauki ba ko kadan - Buhari
Source: UGC

Sai dai Buhari yace duk da babban aikin da ke tattare da hakan, ba zai taba gajiyawa ba wajen fitar da kasar daga kangin da take ciki ba kamar yadda yayi alkawarin kawo karshen cin hanci da rashawa a kasar a 2015.

Hakazalika da yake jawabi, mataimakin Shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo ya soki yadda PDP tayi ta kashe-kashen kudi a shekaru 16 da tayi tana mulki.

KU KARANTA KUMA: APC ta yi mana rashin adalci a Zamfara - Inji Gwamna Yari

A nashi bangaren, Shugaban jam’iyyar APC na kasa, Adams Oshiomhole yace zai zao babban kuskure idan yan Najeriya suka sake zabar dan takarar jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar a zaben ranar 16 ga watan Fabrairu.

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit Newspaper

Tags:
Mailfire view pixel