Zargi: Hadimin Buhari ya bayyana tuggun da Atiku ya kulla idan yayi nasara a zaben 2019

Zargi: Hadimin Buhari ya bayyana tuggun da Atiku ya kulla idan yayi nasara a zaben 2019

- Wani hadimin shugaban kasa Buhari, Sanata Ita Enang, ya ce ba bu wani mafificin zabi da ya wuce Ubangidan sa cikin dukkanin 'yan takarar kujerar shugaban kasa

- Sanata Enang ya ce shugaba Buhari ya na da kosasshiyar lafiya, kuzari gami da karsashi na ci gaba da jagorantar Najeriya tsawon shekaru hudu masu gabatowa

- Hadimin shugaban kasar ya ce sai an kai ruwa rana Atiku zai amince da jagoranci kasar nan a karo daya kacal yayin samun nasara a zaben bana

Sanata Ita Enang, babban hadimi na musamman ga shugaban kasa Muhammadu Buhari akan harkokin da suka shafi majalisar dattawan Najeriya ya ce, ba bu wani mafificin zabi da ya wuce ubangidan sa a yayin babban zabe cikin dukkanin 'yan takarar kujerar shugaban kasa.

Enang yayin neman goyon bayan al'ummar jihar Akwa Ibom, ya nemi da su fito kwansu da kwarkwata domin jefa kuri'un su ga shugaban kasa Buhari yayin babban zabe da zai gudana a ranar 16 ga watan Fabrairu.

Sanata Ita Enang

Sanata Ita Enang
Source: Depositphotos

Kamar yadda kamfanin dillancin labarai na Najeriya ya ruwaito, Sanata Enang ya zayyana hakan ne yayin ganawar sa da manema labarai a mahaifar sa ta garin Idipep da ke karkashin karamar hukumar Ibiomo Ibom ta jihar Akwa Ibom.

Hadimin na musamman ya na ci gaba da kyautata zaton samun nasarar shugaban kasa Buhari yayin babban zaben kasa. Ya ce kwazo gami da bajintar sa a bisa kujerar mulki za ta yi tasiri wajen cancanta gami da tabbatar da nasarar sa a zaben bana.

Ya ke cewa, nasarar Buhari a zaben bana za ta tabbatar da kwarar romon dimokuradiyya ta hanyar ci gaba da ayyukan sa kuma bayan karewar wa'adin sa karagar mulkin kasar nan za ta koma hannun Kudancin Najeriya.

KARANTA KUMA: Yakin Zabe: Ganduje ya rufe dukkanin filayen wasanni yayin da Atiku ya kudiri zuwa Kano

A cewar sa, za a sha fama gami da kai ruwa rana da dan takarar kujerar shugaban kasa na jam'iyyar PDP, Atiku Abubakar, wajen samun amincewar sa ta jagorantar kasar nan a karo daya kacal muddin ya yi nasara a zaben bana.

Ya ce ko kadan guguwar mulki ba za ta taba bari Atiku ya amince da jagorancin kasar nan a karo daya kacal ba. Ya ce manufar su ita ce samun jagora da zai mika akalar mulki a hannun Kudancin Najeriya bayan shekaru hudu ma su zuwa.

Da yake ci gaba da jaddada goyon baya, Sanata Enang ya ce shugaban kasa Buhari yana da kosasshiyar lafiya, kuzari gami da karsashi na ci gaba da jagorantar Najeriya tsawon shekaru hudu masu gabatowa.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na zaurukan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel