APC ta yi mana rashin adalci a Zamfara - Inji Gwamna Yari

APC ta yi mana rashin adalci a Zamfara - Inji Gwamna Yari

- Gwamnan Jihar Zamfara Abdul’aziz Yari uwar jam’iyyar APC da yi wa al’umar Zamfara magoya bayan jam’iyyar rashin adalci

- Yari ya yi wannan furucin ne a cikin wani hira da manema labarai a Abuja

- Gwamnan ya jaddada cewa duk da ran su ya baci, sun yafe wa APC rashin adalcin da ta yi musu

Gwamnan Jihar Zamfara Abdul’aziz Yari, ya bayyana cewa uwar jam’iyyar All Progressives Congress (APC) ta kasa, ta yi wa al’umar Zamfara magoya bayan jam’iyyar rashin adalci.

Yari ya yi wannan furucin ne a cikin wani hira da manema labarai a Abuja, jaridar Premium Times ta ruwaito.

Sai dai kuma ya kara da cewa duk da ran su ya baci, sun yafe wa APC rashin adalcin da ta yi musu.

APC ta yi mana rashin adalci a Zamfara - Inji Gwamna Yari

APC ta yi mana rashin adalci a Zamfara - Inji Gwamna Yari
Source: UGC

Cikin bidiyon dai Yari ya rika kawo ayoyi daga cikin kundin tsarin mulkin Najeriya da ya ce sun nuna halascin zaben fidda gwanin da ya gudanar na APC a jiharsa.

Bayan nan kuma ya sake buga misali da yadda aka fitar da sunan Shugaba Muhammadu Buhari a takarar shugaban kasa, a ka ce an amince shi ne dan takara.

KU KARANTA KUMA: Mun shirya kan mutuwa kan El-Zakzaky – Yan Shi’a

Yari ya ce duk da haka an bi kananan hukumomi da jihohi an yi layin tabbatar da Buhari, sannan aka zo Abuja aka jaddada shi.

A kan haka ya ce ashe kenan su ma abin da suka yi a Zamfara daidai ne kenan.

Gwamnan wanda wa’adin sa ke karewa cikin watan Mayu, ya yi wa jihar fatan alheri da kuma fatan samun shugabanni nagari.

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel