Yakin neman zabe: Jama'ar jihar Ekiti sun nuna wa Buhari kauna, hotuna

Yakin neman zabe: Jama'ar jihar Ekiti sun nuna wa Buhari kauna, hotuna

Dubun dubatar jama'a a jihar Ekiti sun yi tururuwa wajen halartar taron yakin neman sake zaben shugaba Buhari a matsayin shugaban kasar Najeriya a karo na biyu.

A yau, Talata, ne shugaba Buhari tare da tawagar yakin neman zaben jam'iyyar APC su ka dira jihar Ekiti domin kaddamar da yakin neman zaben shugaban kasa.

Ekiti ta dawo hannun jam'iyyar APC ne a zaben gwamnan jihar da aka gudanar a watan Afrilu a shekarar 2018.

Yakin neman zabe: Jama'ar jihar Ekiti sun nuna wa Buhari kauna, hotuna

Jama'ar jihar Ekiti a wurin kamfen din Buhari
Source: Twitter

Yakin neman zabe: Jama'ar jihar Ekiti sun nuna wa Buhari kauna, hotuna

Yakin neman zabe Buhari a Ekiti
Source: Twitter

Yakin neman zabe: Jama'ar jihar Ekiti sun nuna wa Buhari kauna, hotuna

Jama'ar jihar Ekiti sun nuna wa Buhari kauna
Source: Twitter

Yakin neman zabe: Jama'ar jihar Ekiti sun nuna wa Buhari kauna, hotuna

Yakin neman zabe: Jama'ar jihar Ekiti sun nuna wa Buhari kauna
Source: Twitter

Ko a jiya, Litinin, sai da tsofin janar a rundunar soji ta sama, kasa, da ruwa sun bayyana goyon bayan su ga takarar shugaba Buhari domin sake zama shugaban kasar Najeriya a karo na biyu.

DUBA WANNAN: Kamfen: Jama'a sun wulakanta gwamna Badaru na jihar Jigawa

Tsofin janara-janar din sun hada da ma su mukamin manjo janar 13, Air Vice Marshal (AVM) 8, Rear Admiral 2, birgediya janar 12, Air Commodore 9, Commodore 8 da kuma wasu tsofin shugabannin rundunar soji 17.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel