Mun shirya kan mutuwa kan El-Zakzaky – Yan Shi’a

Mun shirya kan mutuwa kan El-Zakzaky – Yan Shi’a

- Yan Shi’a sun kaddamar da cewa sun shirya mutuwa akan shugabansu, Sheikh Ibrahim El-zakzaky

- Sun bayyana hakan a Abuja a ranar Talata, 5 ga watan Fabarairu yayinda suke karade a manyan unguwanin birnin tarayya

Mambobin kungiyar yan uwa Musulmai na Shi’a sun kaddamar da cewa sun shirya mutuwa akan shugabansu, Sheikh Ibrahim El-zakzaky.

Sun bayyana hakan a Abuja a ranar Talata, 5 ga watan Fabarairu yayinda suke karade a manyan unguwanin birnin tarayyar kasar.

Mun shirya kan mutuwa kan El-Zakzaky – Yan Shi’a

Mun shirya kan mutuwa kan El-Zakzaky – Yan Shi’a
Source: Facebook

“Mun shirya mutuwa kan Zakzaky. Ba za su janye ba har sai an saki Shugaban mu da matarsa. Mun shirya mutuwa kan El-zakzzaky.” inji su.

Shugaban kungiyar yan shi’an na fuskantar shari’a na kisa, tayar da zaune saye, tara jama’a ba bisa ka’ida ba, da kuma hana mutane zaman lafiya da dai sauransu.

An fara gurfanar da shi tare da matarsa a ranar 15 ga watan Mayu, 2018 biyo bayan kama su da aka yi a Zaria a watan Disamban 2015.

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: Yan fashi sun kashe yar'uwar Sanata Marafa, sun sace mijinta

A wani lamari na daban, mun ji cewa Joram Van Klaveren, wani dan siyasa kuma mai nuna adawarsa ga addinin musulunci a kasar Holland ya bayar da sanarwar ya musulunta a jiya Litinin, 4 ga watan Fabrairu.

An tattaro cewa Joram ya musulunta ne a lokacin da yake kokarin rubuta littafi don sukar musulunci, da bakinsa ya ce sai ya fahimci wasu abubuwa da suka sanya shi dole ya koma addinin na musulunci kamar yadda ya bayyana a gidan rediyon Ducth.

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel