Yakin Zabe: Ganduje ya rufe dukkanin filayen wasanni yayin da Atiku ya kudiri zuwa Kano

Yakin Zabe: Ganduje ya rufe dukkanin filayen wasanni yayin da Atiku ya kudiri zuwa Kano

Mun samu cewa, yawon yakin neman zabe da kuma karade jihohi 36 na Najeriya wanda dan takarar kujerar shugaban kasa na jam'iyyar PDP ke ci gaba da gudanarwa ya gamu cikas yayin da gwamnan jihar Kano ya dauki wani babban mataki.

Da sanadin kafar watsa labarai ta jaridar Dily Nigerian, mun samu rahoton cewa, gwamnan jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje, ya dauki wani babban mataki cikin salo domin dagula lissafin yakin neman zabe na babbar jam'iyyar adawa ta PDP.

Rahotanni kamar yadda majiyar jaridar Legit.ng ta ruwaito sun bayyana cewa, gwamnan jihar Kano ya bayar da umarnin rufe dukkanin filayen wasanni yayin da ya rage sauran kwanaki 6 jam'iyyar PDP ta gudanar da taron ta na yakin neman zabe a tsohon birnin na Kanon Dabo.

Ganduje cikin shirin tarbar shugaba Buhari yayin yakin zaben sa a jihar Kano

Ganduje cikin shirin tarbar shugaba Buhari yayin yakin zaben sa a jihar Kano
Source: Twitter

Ko shakka ba bu bincike ya tabbatar da cewa, Atiku Abubakar, dan takarar kujerar shugaban kasa tare da tawagawar sa ta jiga-jigan jam'iyyar PDP sun kudiri aniyyar gudanar da taron su na yakin neman zabe cikin harabar filin wasanni ta Sani Abacha ko kuma filin wasanni na Kano Pillars da ke tantagwaryar birnin Kano.

A sanadiyar tsantsar adawa ta siyasa, gwamnan jihar ya bayar da umarni ga ma'aikatar kula da harkokin wasanni ta jihar akan gaggauta rufe filayen wasannin biyu domin gudanar da wasu ayyuka na gyare-gyare da inganta gine-ginen su.

Wata majiyar rahoto da ke dangantuwa zuwa fadar gwamnatin jihar, ta bayar da tabbacin cewa gwamna Ganduje ya dauki wannan babban mataki cikin salo domin dagula lissafin da kuma tsare-tsaren gudanar da taron yakin neman zabe na jam'iyyar PDP a jihar.

Bayan bege na sakaya sunanta majiyar rahoton ta kuma bayyana cewa, gwamna Ganduje ya dauki wannan mataki cikin gaggawa yayin samun rahoton irin dumbin al'umma magoya baya da za su halarcin taron yakin zaben a jihar sa.

KARANTA KUMA: Cikin Hotuna: Atiku da jiga-jigan PDP sun ziyarci fadar Sultan na Sakkwato

Ta ke cewa, baya ga gajiyawar al'umma da mulkin Ganduje a jihar Kano, akwai kuma yiwuwar Atiku zai tara adadin al'umma magoya baya fiye da wadda shugaban kasa Muhammadu Buhari ya tara yayin yakin zaben sa da ya gudanar cikin jihar a makon da ya gabata.

Yayin tuntubar kakakin cibiyar kula da harkokin wasanni na jihar Kano, Abbati Sabo, ya musanta wannan zargi da cewar gwamna Ganduje ba ya da wata manufa ta dagula shirin jam'iyyar PDP a yayin da za ta gudanar da taron ta na yakin zabe.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na zaurukan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel