INEC: Ko ta kaka sai mun gudanar da zabe a Madagali da Michika

INEC: Ko ta kaka sai mun gudanar da zabe a Madagali da Michika

Hukumar gudanar da zabe ta kasa mai zaman kanta wato INEC ta bayyana cewa harin da yan Boko Haram suka kai karamar hukumar Madagali ba zai hanasu gudanar da zaben shugaban kasa da sauran a jihar Adamawa.

Kwamishanan hukumar INEC na jihar, Mista Kasin Gaidam, ya bayyanawa manema labarai cewa shirye suke da gudanar da zabe a wurare daban-daban a Madagali.

Yace: "Hukumar gudanar da zabe ta kasa mai zaman kanta, al'ummar garin Madagali da jama'ar jihar Adamawa gaba daya sun yi ittifaki kan gudanar da zabe a Madagali."

"Komin barazana, tashi hankali, da yaudara ba zai hana INEC gudanar da zabe ba."

Kwamishanan ya kara da cewa da goyon bayan jami'an tsaro da masu ruwa da tsaki, za su tabbatar an gudanar da zabe cikin zaman lafiya da lumana.

Gaidam ya ce akalla mutane 81,000 sukayi rijistan zabe a karamar hukumar Madagali, saboda haka ba zai dace a waresu ba.

Mun kawo muku rahoton cewa Mazauna karamar hukumar Madagali da Michika na jihar Adamawa sun fara komawa muhallansu bayan kimanin sa'o'i 24 da suka gudu daga gidajensu sakamakon harin Boko Haram da suka kawo yammacin Litinin.

Kwamishanan yada labarai na jihar Adamawa, Malam Ahmad Sajoh, ya bayyanawa manema labarai cewa jami'an tsaron sun dakile harin da yan ta'addan suka kawo.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel