Asha: An samu bullar wata cutar huhu mai yaduwa a jihar Kaduna

Asha: An samu bullar wata cutar huhu mai yaduwa a jihar Kaduna

Gwamnatin jihar Kaduna ta sanar da bular wata cutar dabobi mai yaduwa da ake tsamanin cutar huhu ne mai suna Contagious Bovine Pleuro Pneumonia, CBPP da ke kashe shanu a jihar.

Jami'in hulda da Jama'a na ma'aikatan Noma da Gandun Daji na jihar, Dahiru Abdullahi ne ya sanar da bullar cutar a wani hirar tarho da ya yi da kamfanin dillancin labarai na kasa NAN.

Mr Abdullahi ya ce, "an samu bullar wata cuta da ba a gano kanta ba a wasu sassan jihar.

"Likitocin dabobi na ma'aikatan sun fara daukan jinin dabobin da suka mutu domin yin gwaji a dakin bincike saboda a gano ko wane irin cuta ne."

Asha: An samu bullar wata cutar huhu mai yaduwa a jihar Kaduna

Asha: An samu bullar wata cutar huhu mai yaduwa a jihar Kaduna
Source: Depositphotos

NAN ta ruwaito cewa an samu bullar cutar a wasu garuruwa a kananan hukumomin Kachia, Kagarko da Anchau.

Wani bafulani mai kiwo, Suleiman Adamu ya shaidawa NAN cewa a halin yanzu cutar da kashe fiye da shanu 100 a garkensu da ke mazabar Doka a karamar hukumar Kachia cikin makonni uku.

Adamu ya ce mahaifinsu, Alhaji Dano da ke da shanu fiye da 500 yana cikin fargabar da tsoro sakamakon bullar cutar.

Ya nuna damuwarsa kan abinda ya kira tafaiyar hawainiya da gwamnati keyi wurin daukan mataki a kan cutar da ke cigaba da yaduwa.

NAN ta ruwaito cewar shanun da suka kamu da CBPP ba su iya numfashi cikin sauki wadda hakan babban matsala ce a gare su.

Sauran alamomin cutar kamar yadda kwararu a kan CBPP suka fadi sun hada da tari musamman idan dabar tayi tafi ko an saka ta gudu.

Dabobin da suka kamu da cutar su kan rame sosai tare da gurnani idan an taba kirjinsu, sannan suna fama da zazabi da mura da wasu alamomin.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel