Na yi da-na-sanin goyon bayan Oshiomhole har ya zama shugaban APC na kasa - Okorocha

Na yi da-na-sanin goyon bayan Oshiomhole har ya zama shugaban APC na kasa - Okorocha

- Rochas Okorocha, ya bayyana da-na-saninsa na goyon bayan Adams Oshiomhole a lokacin da ya zama shugaban jam'iyyar APC na kasa

- Gwamna Okorocha, ya ce ya goyi bayan shugaban jam'iyyyar ne ba tare da ya san ainihin ma'anar sunan ba

- Ya ce Nzeribe, Izunaso da Hope Uzodinma sun bata lokaci da shekaru masu tsawo ba tare da sun kawo wani abun azo a gani a mazabar Orlu ba

Gwamnan jihar Imo, Rochas Okorocha, ya bayyana da-na-saninsa na goyon bayan Adams Oshiomhole a lokacin da ya zama shugaban jam'iyyar All Progressives Congress, (APC) na kasa.

Gwamnan, wanda ya bayyana hakan a filin wasanni na Orlu a yayin kaddamar da yakin zabensa na kujerar sanatan mazabar Orlu a zabe mai zuwa, ya ce ya goyi bayan shugaban jam'iyyyar ne ba tare da ya san ainihin ma'anar sunan ba.

Okorocha ya ce saukarsa daga kujerar gwamnan jihar ba wai yana nufin kawo karshen siyasarsa ba, yana mai cewa: "Kawo karshen wa'adin shugabancin jihar ba wai alamar karshe a siyasata bane. Kamar dai wakafi ne bayan kowanne wakafi, tabbas, akwai jimla da zata biyo bayan wakafin.

KARANTA WANNAN: Da duminsa: An kashe mutane biyu a yayin da El-Rufai ya fita yakin zabe a Kaduna

Na yi da-na-sanin goyon bayan Oshiomhole har ya zama shugaban APC na kasa - Okorocha

Na yi da-na-sanin goyon bayan Oshiomhole har ya zama shugaban APC na kasa - Okorocha
Source: Depositphotos

"Wadanda suke jin tsoro na, a siyasance, sun yi gangami domin yakata, wanda ya hada da wanda na goyi baya har ya zama shugaban jam'iyyar na kasa. Wannan ne ya sa suka kawo maku Hope Uzodinma. Ba wai ya zo bane domin yin takarar siyasa kadai ba, ya zo ne domin ya yi fada da ni."

"Haka zalika ina neman takarar sanatan wannan mazabar tawa ne domin idan har na je majalisar dattijai, zan kawo abubuwan ci gaba masu yawa ga al'ummar mazabar Orlu. Kun dai ga irin ayyukan da na gudanar a lokacin da nake gwamna. Idan na je majalisa, za ku ga banbanci sosai.

"Nzeribe, Izunaso da Hope Uzodinma sun bata lokaci da shekaru masu tsawo ba tare da sun kawo wani abun azo a gani a mazabar Orlu ba. Su burinsu aljihunansu ne kawai ba wai jama'ar garin ba."

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel