Yanzu-yanzu: Ana saura yan kwanaki zabe, kotu ta sallami dan takarar gwamnan APC

Yanzu-yanzu: Ana saura yan kwanaki zabe, kotu ta sallami dan takarar gwamnan APC

Wata babban ktun tarayya dake zaune a birnin tarayya Abuja ta sallami Sanata Ayogu Eze a matsayin dan takaran gwamnan jihar Enugu karkashin jam'iyyar All Progressives Congress, APC.

A wata shari'a da ya yanke a ranan Talata, 5 ga watan Febrairu, Alkali mai shari'a, Jastis I Ekwo ya umurci hukumar gudanar da zabe ta kasa mai zaman kanta wato INEC ta maye sunan Ayogu Eze da Barista George Ogara.

Ya caccaki kwamitin da uwar jam'iyyar APC ta turo gudanar da zaben fidda gwani a jihar Enugu.

Wanda kotu ta tabbatar, George Ogara, ya bayyanawa manema labarai cewa wannan nasara ce ga al'umma.

Yace: "Mun godewa Allah da kawo adalci daga karshe. Ina kira ga mambobi jam'iyyarmu sun kasance tsintsiya yayinda zamu samu nasara a zabe mai zuwa."

Ku saurari karin bayani....

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel