Dan siyasa mai kyamar Musulunci a Holland ya amshi Musulunci

Dan siyasa mai kyamar Musulunci a Holland ya amshi Musulunci

- Wani dan siyasa kuma mai nuna adawarsa ga addinin musulunci a kasar Holland ya amshi Musulunci

- Joram ya musulunta ne a lokacin da yake kokarin rubuta littafi don sukar musulunci

- Ya ce ya fahimci wasu abubuwa da suka sanya shi dole ya koma addinin na Islama

Rahotanni sun kawo cewa Joram Van Klaveren, wani dan siyasa kuma mai nuna adawarsa ga addinin musulunci a kasar Holland ya bayar da sanarwar ya musulunta a jiya Litinin, 4 ga watan Fabrairu kamar yadda majiyarmu ta nishadi TV ta ruwaito.

An tattaro cewa Joram ya musulunta ne a lokacin da yake kokarin rubuta littafi don sukar musulunci, da bakinsa ya ce sai ya fahimci wasu abubuwa da suka sanya shi dole ya koma addinin na musulunci kamar yadda ya bayyana a gidan rediyon Ducth.

Dan siyasa mai kyamar Musulunci a Holland ya amshi Musulunci

Dan siyasa mai kyamar Musulunci a Holland ya amshi Musulunci
Source: UGC

Joram Van Klaveren dai dan jam'iyyar PVV ne daga 2010 zuwa 2014 inda ya bar jam'iyyar sanadiyyar da ya ga akwai magoya bayan jam'iyyar da dama da suka zo daga kasar Marocco.

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: Yan fashi sun kashe yar'uwar Sanata Marafa, sun sace mijinta

A lokacin da yake jam'iyyar PVV ya taba cewa addinin musu;lunci karya ce kawai, kuma Alkur'ani guba ce.

Da aka tambaye shi ko zai iya tuna wadannan kalamai da ya fada game da musulunci bayan ya musulunta sai ya ce kawai goguwar adawar siyasa ce irin ta PVV.

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel