El-Rufai a matse yake daya murde zaben nan ko ta halin qaqa - Hadakar jam'iyyun adawa

El-Rufai a matse yake daya murde zaben nan ko ta halin qaqa - Hadakar jam'iyyun adawa

- Jam'iyar CUPP tana zargin gwamna Nasir El rufa'i da yin amfani da jiharsa wajen yin magudi a zabe mai zuwa

- Suna zargin nasa ne bisa ga sabuwar kwamitin samar da tsaro daya kafa

- CUPP tace El rufa'i yanata kokarin cusawa hukumar yansanda mutanen sa wadanda akafi sani da "Kato da gora" dansu kasance masu bada tsaro a wajen zabe

El-Rufai a matse yake daya murde zaben nan ko ta halin qaqa - Hadakar jam'iyyun adawa

El-Rufai a matse yake daya murde zaben nan ko ta halin qaqa - Hadakar jam'iyyun adawa
Source: UGC

A ranar Talata ne jam'iyyar CUPP ta bayyana zargin da takeyiwa gwamnan jihar Kaduna Mal.Nasir El rufa'i na kokarin yin magudi a zabe mai zuwa.

Jam'iyar ta bayyana hakan ne a wani taro da tayi a Kaduna inda tace El-rufai na kokarin juya lamarin zaben jihar ta hanyar samar da wata sabuwar kwamitin tsaro daya kafa wanda yakeso su bada kariya a wajen kada kuri'a.

GA WANNAN: Ranar da na bar PDP a ranar ta mutu murus! Inji Sanata Akpabio

Ciyaman na jam'iyar ta CUPP Hon Umar Ibrahim Mairakumi ya bayyana cewa gwamnan yana ta kokarin ganin hukumar yansanda da hukumar zabe INEC sun amince da kudirin sa na sanya yan "Kato da Gora" a cikin wadanda zasu bada gudummawa a wajen zabe.

Mairakumi yayi kira ga hukumomin tsaro da INEC dasu tabbatar sun bada kulawar data kamata a zaben dazai gudana.

A wani bangaren kuma El rufa'i da dan takarar gwamna a jami'yar PDP da ragowar yan takara sun sanya hannu akan yarjejenir zaman lafiya a zaben dazai gudana.

Yan takarar sun sanya hannun ne a hedkwatar hukumar yan sandan jihar Kaduna.

Kwamishinan yan sandan jihar Cp Ahmed Abdulrahman ya tabbatar da cewa hukumomin tsaro zasuyi aiki yanda ya kamata dan samar da ingantaccen zabe.

Shafin NAIJ.com Hausa ne ya koma LEGIT.ng Hausa

Latsa kuga sabuwar manhajar Legit.ng Hausa a wayarku ta salula: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafukanmu na dandalin sada zumunta sune:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel