An sace wa bulaliyar majalisar Katsina diya da wasu su biyu, ko fansa ko kazamar siyasa

An sace wa bulaliyar majalisar Katsina diya da wasu su biyu, ko fansa ko kazamar siyasa

- Masu yin garkuwa da mutane sun dauke matar dan majalisar jihar Katsina da yar sa

- Masu garkuwar sun so sace mijinta ne amma basu sameshi ba

- Sun sace 'ya'yan wani likita guda Biyu inda suka nemi a basu N100m

An sace wa bulaliyar majalisar Katsina diya da wasu su biyu, ko fansa ko kazamar siyasa

An sace wa bulaliyar majalisar Katsina diya da wasu su biyu, ko fansa ko kazamar siyasa
Source: Facebook

Wasu masu garkuwa da mutane sun sace matar dan majalisar jihar Katsina Bello Abdu Danmusa da yar sa.

Hajiya Amina Danmusa ta auri wani mai suna Miftahu Yakubu Ciro a garin danmusa inda a nan ne lamarin ya afku.

Wadanda lamarin ya afku a gabansu sun bayyana cewa masu garkuwar sun kawo farmaki ne a kokarin su nayin garkuwa da mijinta amma saiya kasance bayanan.

Sannan sunso daukar wata dattijuwa da ake kira da Baba maiwaina bayan ta samu raunika.

GA WANNAN: Jam'iyyar AA ta Rochas a Imo, ta fara aikin ganin shugaba Buhari ya zarce a wannan watan

Masu garkuwar sun dauki 'ya'yan wani likita guda biyu mai suna Dr MJ Yusuf a garin Jibia.

Sun dauki yaran ne tare da mahaifiyar a cikin dare da musalin 1am inda ita uwar ta samu nasarar fadowa daga cikin motar su sai sukayi gaba da yaran.

Masu garkuwar sun nemi a basu N100m dansu saki yaran.

Jami'an 'yansanda suna cigaba da bincike akan afkuwar wadannan lamura guda Biyu.

Shafin NAIJ.com Hausa ne ya koma LEGIT.ng Hausa

Latsa kuga sabuwar manhajar Legit.ng Hausa a wayarku ta salula: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafukanmu na dandalin sada zumunta sune:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel