Da duminsa: An kashe mutane biyu a yayin da El-Rufai ya fita yakin zabe a Kaduna

Da duminsa: An kashe mutane biyu a yayin da El-Rufai ya fita yakin zabe a Kaduna

Rahotannin da Legit.ng Hausa ta samu daga jaridar Daily Trust na nuni da cewa an kashe wasu mutane biyu a Unguwar Mu'azu, da ke cikin kwaryar Kaduna, a yayin da wasu gungun matasa suka yi artabu a ranar Litinin, lokacin da Gwamna Nasir El-Rufai ya je yankin domin kaddamar da yakin zabensa.

Rahotannin sun bayyana cewa a yayin da gwamnan ke gabatar da jawabinsa a gaban taron jama'ar a makarantar Firamare ta Unguwar Mu'azu, an jiyo wasu matasa na ihu da kuma farwa junansu, nesa kadan da filin yakin zaben.

Sai dai har yanzu ba a tabbatar da cewa ko mutanen suna daga cikin mahalarta taron yakin zabensa ba, amma wanda lamarin ya afku a gabansa ya shaidawa jaridar Daily Trust cewa gungun matasan sun yi amfani da muggan makamai kamar manyan wukake, adduna da sauransu, inda daga bisani jami'an tsaro suka fatattake su tare da hadin guiwar jami'an sa kai na JTF.

KARANTA WANNAN: Assha: Tsohon DCG hukumar kwastan ya gamu da ajalinsa a hannun 'yan bindiga

Da duminsa: An kashe mutane biyu a yayin da El-Rufai ya fita yakin zabe a Kaduna

Da duminsa: An kashe mutane biyu a yayin da El-Rufai ya fita yakin zabe a Kaduna
Source: Facebook

Baban Khalifa, wanda ya ganewa idanuwansa rikicin, ya ce: "Muna filin yakin zaben sai muka fara jiyo ihun matasa suna rikici. Mun ji cewa sun fito ne daga bangarorin Yan tsulhu da Ba tsulhu.

"Muna sai muka fara guduwa saboda ganin yadda matasan ke wasa da wukake da addunan suna saran junansu. In takaita maka, a cikin hakan ne ma aka kashe mutane guda biyu," a cewarsa.

Shi ma wani ganau, wanda ya bukaci a sakaya sunansa, ya fadi sunan daya daga cikin wadanda aka kashe mai shekaru 22 da suna Salihu, wanda ya ke gyaran ababen hawa a yankin.

Su dai wadannan bangarori biyu na Yan tsulhu da Ba tsulhu, sun kasance kungiyoyin da suka fitini mazauna kwaryar jihar. Da yawan lokuta, suna kaiwa junansu hare hare, inda har sukan hada da kan mai uwa da wabi.

Duk wani yunkuri na jin ta bakin jami'in hulda da jama'a na rundunar 'yan sanda na jihar, Yakubu Sabo ya ci tura, har zuwa lokacin kammala rubuta wannan labari.

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel