Yanzu Yanzu: Yan fashi sun kashe yar'uwar Sanata Marafa, sun sace mijinta

Yanzu Yanzu: Yan fashi sun kashe yar'uwar Sanata Marafa, sun sace mijinta

- Wasu yan fashi da makami sun kashe Ade Marafa, babbar yayar Kabir Marafa, Sanata mai wakiltan Zamfara ta tsakiya

- Sun kuma tafi da mijin marigayiyar zuwa wani wuri da ba a sani ba

- Yan fashin sun kai farmaki gidan yayar sanatan da ke Ruwan Bore na karamar hukumar Gusau a ranar Talata, 5 ga watan Fabrairu sannan sun cinna ma kauyen wuta

Wasu yan fashi da makami sun kashe Ade Marafa, babbar yayar Kabir Marafa, Sanata mai wakiltan Zamfara ta tsakiya, sannan suka sace mijinta.

Abubakar Tsafe, wani hadimin sanatan wanda ya tabbatar da lamarin yace yan fashin sun kai farmaki gidan yayar sanatan da ke Ruwan Bore na karamar hukumar Gusau a ranar Talata, 5 ga watan Fabrairu.

Hadimin ya bayyana cewa yan fashin da yawansu ya kai 100 sun sanya ma kauyen wuta bayan harin.

Hadimin nasa yace: “Yan fashin sun kona sama da rabin kauyen Ruwan Bore. A yanzu haka yan kauyen na zaune a Mada, wani kauye da ke makwabtaka da su.”

KU KARANTA KUMA: Har yanzu ba a daina karkatar da kudaden jama’a a gwamnati na ba - Buhari

Ya ci gaba da cewa a yanzu ba a san inda surikin sanatan yake ba tukuna.

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel