Cikin Hotuna: Atiku da jiga-jigan PDP sun ziyarci fadar Sultan na Sakkwato

Cikin Hotuna: Atiku da jiga-jigan PDP sun ziyarci fadar Sultan na Sakkwato

Da misalin karfe 11.00 na daren jiya Litinin 4 ga watan Fabrairu, Atiku Abubakar, dan takarar kujerar shugaban kasa tare da tawagar jiga-jigan jam'iyyar PDP, sun ziyarci fadar mai martaba Sarkin Musulmi, Sultan Sa'ad Abubakar.

Atiku yayin dirar sa a birnin Shehu tare da gwamna Aminu Tambuwal na jihar Sakkwato

Atiku yayin dirar sa a birnin Shehu tare da gwamna Aminu Tambuwal na jihar Sakkwato
Source: Twitter

Gwamna Tambuwal cikin fara'a yayin dawowar su daga jihar Zamfara

Gwamna Tambuwal cikin fara'a yayin dawowar su daga jihar Zamfara
Source: Twitter

Atiki yayin kwarara jawabai a fadar Sultan na Sakkwato

Atiki yayin kwarara jawabai a fadar Sultan na Sakkwato
Source: Twitter

Atiku, Tambuwal, shugaban jam'iyyar PDP; Secondus tare da Sultan na Sakkwato

Atiku, Tambuwal, shugaban jam'iyyar PDP; Secondus tare da Sultan na Sakkwato
Source: Twitter

Gwamna Tambuwal yayin gabatar jawabai a fadar Sultan na Sakkwato

Tawagar Atiku a fadar Sultan na Sakkwato

Tawagar Atiku a fadar Sultan na Sakkwato
Source: Twitter

Tawagar Atiku a fadar Sultan na Sakkwato

Tawagar Atiku a fadar Sultan na Sakkwato
Source: Twitter

Atiku, Tambuwal, shugaban jam'iyyar PDP; Secondus tare da Sultan na Sakkwato

Atiku, Tambuwal, shugaban jam'iyyar PDP; Secondus tare da Sultan na Sakkwato
Source: Twitter

Mun samu cewa, Atiku da shugabannin jam'iyyar sa ta PDP sun ziyarci fadar mai martaba Sultan na Sakkawato bayan sun gudanar da taron yakin neman zaben kujerar shugaban a birnin Gusau na jihar Zamfara.

Cikin zayyana jawaban sa, Sultan ya gargadi dukkanin 'yan siyasa da suka mike tsaye tukuru tare da zage dantse da kuma daura damarar tunkarar matsalolin tsaro da kasar ke fuskanta, rashin aikin yi da kuma talauci da suka yiwa kasar nan katutu.

KARANTA KUMA: Ba bu wani rikici akan kudin yakin zabe - PDP

Sultan Sa'ad ya kuma nemi 'yan siyasa da su jajirce wajen tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankalin al'umma yayin gudanar da babban zabe a fadin kasar nan tare da shawartar kan muhimmancin cika alkawurran su yayin samun nasara ta hayewa bisa karagar mulki.

Ya kuma nemi hukumomin tsaro da suka kauracewa shiga cikin harkokin da mu'amala ta nuna ra'ayi na akidar siyaya yayin sauke nauyin da rataya a wuyan su wajen tabbatar an gudanar da zabe cikin kwanciyar hankali da lumana.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na zaurukan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel