Nayi nadamar goyon bayan Oshiomhole a matsayin Shugaban APC - Okorocha

Nayi nadamar goyon bayan Oshiomhole a matsayin Shugaban APC - Okorocha

- Gwamna Rochas Okorocha na jihar Imo ya ce ya yi nadamar goyon bayan da ya bawa Shugaban APC, Adams Oshiomhole

- Gwamna Okorocha ya yi zargin cewa Oshiomhole yana daga cikin 'yan siyasar da ke masa zagon kasa

- Gwamnan na jihar Imo ya ce ya yanke shawarar takarar Sanata ne saboda ya samar da abubuwan more rayuwa ga mutanen Orlu

An ruwaito cewar Gwamna Rochas Okorocha ya ce ya yi nadamar marawa Adams Oshiomhole baya gabanin zaman shugaban jam'iyyar APC na kasa.

Gwamnan mai barin gado wadda kuma shine dan takarar kujerar Sanata na yankin Imo ta Yamma ya yi wannan maganar ne a filin wasanni na Orlu a ranar Litinin 4 ga watan Fabrairu inda kuma ya yi zargin cewa Oshiomhole yana cikin 'yan siyasar da ke masa buqulu a siyasa kamar yadda The Guardian ta ruwaito.

Nayi nadamar goyon bayan Oshiomhole a matsayin Shugaban APC - Okorocha

Nayi nadamar goyon bayan Oshiomhole a matsayin Shugaban APC - Okorocha
Source: UGC

DUBA WANNAN: Jigawa ta cika makil da jama'a da suka fito tarbar Buhari, hotuna

"Sauka ta daga mukamin gwamna ba shine karshen ba. Wadanda ke tsoro na a siyasance sun hada kai suna yi min buqulu cikinsu har da wanda na marawa baya na zama shugaban jam'iyya na kasa. Shi yasa suka kawo Hope Uzodinma. Ba wani zaben da zai yi, an kawo shi ne kawai domin ya yi yaki da ni a mazabar Orlu," inji Rochas.

Ya ce ya yi niyyar yin takarar kujerar sanata ne domin ya cigaba da samarwa mutanen Orlu romon demokradiyya kamar yadda ya yi a lokacin da ya ke gwamna.

"Idan na tafi majalisar dattawa, zaku ga banbanci... Nzeribe, Izunaso da Uzodinma sun mata shekaru bakwai ne amma babu wani aiki da suka kawo wa mutanen mazabar Orlu. Aljihunsu ne kawai abinda suka damu da shi.

"Ku tambayi Osita Izunaso abinda ya yiwa mutanen Orlu a shekaru hudu da ya yi a majalisar wakilai da kuma shekaru hudu da ya yi a matsayin sanata ko gida guda bai ginawa mazabar Orlu ba. Saboda haka ya tafi ya zauna."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel