Ana neman Atiku ruwa a jallo a kasar Amurka – APC ta dauki zafi

Ana neman Atiku ruwa a jallo a kasar Amurka – APC ta dauki zafi

- Jam’iyyar APC tace ana neman Atiku ruwa a jallo a kasar Amurka sannan kuma cewa lasisin shiga Amurka na wucin-gadi aka bashi

- APC tace ta san cewa Amurka ba za ta taba jayayya da tsarin damokradiyar kasarta, take doka da kuma rashin adalci ba

- Jam’iyyar mai mulki tace ta san cewa kwanaki Atiku kirgagu ne, kuma zai tsinci kansa imma a kotun Amurka, Ingila ko Najeriya

Jam’iyyar All Progressives Congress (APC) ta bayyana tafiyar da dan takarar Shugaban kasa a karkashin jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP), Alhaji Atiku Abubakar, yayi zuwa Amurka a kwanakin baya a matsayin wani yunkuri na yaudarar yan Najeriya.

A wani hiran wayar tarho da jaridar Daily Trust, babban sakataren APC na kasa, Malam Lanre Issa-Onilu, ya bayyana cewa rahotannin kwanan nan ya nuna cewa an dai ba Atiku lasisin shiga Amurka na wucin-gadi ne.

Ana neman Atiku ruwa a jallo a kasar Amurka – APC ta dauki zafi

Ana neman Atiku ruwa a jallo a kasar Amurka – APC ta dauki zafi
Source: Depositphotos

Legit.ng ta tattaro cewa Issa-Onilu yace APC ta san cewa Amurka ba za ta taba jayayya da tsarin damokradiyar kasarta, take doka da kuma rashin adalci ba.

Yace: “Ya nuna cewa bamu taba shakkar cewa ana neman Atiku a kasar Amurka ba. Don haka ziyarar da ya kai kasar mun san cewa duk a cikin tsananakin son yaudarar yan Najeriya ne. Don haka bai dame mu ba.

KU KARANTA KUMA: Mambobin SDP da PDP 2,000 sun sauya sheka tare da tsohon mataimakin gwamnan Ondo zuwa APC

“Kuma mun san cewa Amurka ba za ta taba taka manufofin damokradiya, doka da rashin adalci ba. Kwanaki Atiku kirgagu ne. Zai tsinci kansa imam a kotun Amurka, Ingila ko Najeriya.”

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel