Sojoji sun halaka yan bindiga 9, sun ceto mutanen da suka yi garkuwa dasu guda 2 a Zamfara

Sojoji sun halaka yan bindiga 9, sun ceto mutanen da suka yi garkuwa dasu guda 2 a Zamfara

Dakarun rundunar Sojin Najeriya dake gudanar da aikin tabbatar da tsaro a jahar Zamfara sun samu nasarar halaka wasu gagga gaggan yan bindiga guda tara, tare da kama wasu guda biyar, sa’annan suka banka ma sansanoninsu wuta.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito a yayin samamen da suka kai, Sojojin Najeriya tare da hadin gwiwar wasu hukumomin tsaro da kungiyoyin matasan sa kai na jahar Zamfara sun ceto mutane biyu da yan bindigan suka yi garkuwa dasu.

KU KARANTA: Ke duniya ina zaki damu? Wani Uba ya binne dan jariri da ransa a jahar Jigawa

Mukaddashin kakaakin rundunar, Manjo Clement Abiade ne ya bayyana haka cikin rahoton daya fitar na ayyukan da rundunar ta gudanar a cikin makon data gabata, inda Sojojin sun kai samame a Shinkafi, Birnin Magaji, dajin Sunke, Safana, Runka da Kunkan Sama.

Kaakakin ya kara da cewa sun kama wasu yan bindga guda shida tare da wani direban Tanka dake kai musu man fetir a cikin dajin a Gando, a Kwanar Mayanchi, daga cikin abubuwan da suka kwato daga hannunsu akwai alburusai, babur, kwayoyi, galan 45 na man fetir, duro 7 na mai, motar Tanka da injin ban ruwa.

Haka zalika rundunar ta kama wasu mutane guda biyu dake yi ma yan bindiga aiki, Yusuf Mohammed da Abubakar Dabo, a dajin Kwanar Maj-Sunke, inda suka kamasu dauke da miyagun kwayoyi da dama, a yanzu haka sun mikasu ga hukumomin da suka dace domin fara bincike.

Daga karshe Manjo Abiade ya jaddada manufar rundunarsu ta kakkaabe ragowar yan bindiga dake addabar jihohin Zamfara da Katsina, tare da shawo kan munanan miyagun ayyuka da suke tafkawa a jihohin biyu.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel