Da mulkinka ai gwara ma na Abacha sau dubu – Oshiomhole ya caccaki Obasanjo

Da mulkinka ai gwara ma na Abacha sau dubu – Oshiomhole ya caccaki Obasanjo

- Kwamrad Adams Oshiomhole, ya bayyana cewa tsohon Shugaban kasa Olusegun Obasanjo ya fi marigayi Janar Sani Abacha muni

- Obasanjo ya zargi shugaba Buhari da mayar da Najeriya zuwa lokacin da makiyan gwamnati ke yaki da hukumomin kasar

- Oshiomhoe ya nuna rashin amincewa da batun cewa kasar ta koma ta zalunci

Kwamrad Adams Oshiomhole, Shugaban jam’iyyar All Progressives Congress (APC), ya bayyana cewa tsohon Shugaban kasa Olusegun Obasanjo ya fi marigayi Janar Sani Abacha muni.

Oshiomhole ya bayyana hakan a lokacin wata hira da Channels TV, yayinda yake martani ga wani furucin tsohon Shugaban kasar na kwanan nan, da yake zargin Shugaban kasa Muhammadu Buhari da mayar da kasar kamar mulkin Abacha.

Legit.ng ta kawo cewa Obasanjo an wani sanarwa da ya saki, ya zargi shugaba Buhari da mayar da Najeriya zuwa lokacin da makiyan gwamnati ke yaki da hukumomin kasar.

Da mulkinka ai gwara ma na Abacha sau dubu – Oshiomhole ya caccaki Obasanjo

Da mulkinka ai gwara ma na Abacha sau dubu – Oshiomhole ya caccaki Obasanjo
Source: Depositphotos

A cewar Obasanjo, Buhari na aikata darasan da ya koya daga marigayi tsohon Shugaban kasar.

Yace: “A yau mun sake komawa wani mulki na Abacha. Ana amfani da hukumomin tsaro wajen yakar dukkanin masu adawa da yan adawan Buhari da kuma sabawa damokradiyar kasarmu.”

Da yake martani, Oshiomhole ya nuna rashin amincewa da batun cewa kasar ta koma ta zalunci.

KU KARANTA KUMA: Zabe: An gano wasu mutane da ke shirin tayar da husuma

Yace: “Obasanjo ba zai iya duba idanuna ya fadi wadannan abubuwan ba. Ya fi Abacha muni da zalunci.”

Shugaban APC ya kuma yi Magana akan halin da kasar ke ciki. Yace mutane “na fadin cewa Buhari ya gyara Najeriya cikin shekara uku da rabi”alhalin Obasanjo da yayi mulkin shekara takwas ya kasa gyara kasar.

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel