Jarumta: Dakarun soji sun hana Boko Haram rawar gaban hantsi a Yobe

Jarumta: Dakarun soji sun hana Boko Haram rawar gaban hantsi a Yobe

Hukumar Sojin Najeriya ta ce dakarun ta na 159 bataliya sun dakile wata hari da mayakan Boko Haram su kayi yunkurin kaiwa a garin Kanana da ke karamar hukumar Yunusari da ke Jihar Yobe.

A cewar Kakakin hukumar sojin, Injoka Irabo, 'yan ta'addan sun kai farmakin ne a yammacin jiya Litinin a garin Kanama da ke kan iyaka inda suka fara harbe-harbe sai dai dakarun sojojin su kayi wuf suka katse musu hanzari.

A cikin sanarwar da muka samu daga Premium Times, Kakakin sojin ya ce duk da cewa sojoji biyu sun jikkata, dakarun sojin sun yiwa 'yan ta'addan babban illa inda suka kashe da dama a cikinsu.

Dakarun soji sun dakile harin Boko Haram a Yunusari

Dakarun soji sun dakile harin Boko Haram a Yunusari
Source: UGC

Ya ce 'yan ta'addan sun yabawa ayya zaki a hannun dakarun sojojin.

DUBA WANNAN: EFCC: Shaida ya bayyana yadda Shekarau da wasu mutane 2 suka kasafta N950m

"Dakarun soji na 159 bataliya ta Foward Operational Base (FOB), sector 2 na Operation Lafiya Dole da ke sansanin garin Kanama a karamar hukumar Yunusari a jihar Yobe sun dakile harin mayakan Boko Haram da su kayi kokarin shiga garin Kanama da ke kan iyaka a yammacin ranar Litinin.

"Yan ta'addan sun shigo garin misalin karfe biyar da rabi na yamma inda suka fara harbe-harbe sai dai dakarun sojojin na FOB da ke cikin shiri sun taka musu birki.

"Daga bisani sojojin tare da taimakon dakarun sojojin sama na Operation Lafiya Dole sun ci galaba a kan 'yan ta'addan inda suka kashe wasu dama sannan wasu sun tsere da raunin harsashi.

"Jaruman dakarun sojin sun bi bayan 'yan ta'addan har zuwa kan iyakar Jamhuriyar Nijar amma biyu daga cikin sojojin sun samu rauni sai dai suna nan da ransu kuma suna murmurewa a asibitin soji," inji sanarwar.

Mr Irabo ya kara da cewa za a fitar da cikaken bayanin 'yan ta'addan da aka kashe da makaman da aka kwato a nan gaba.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel