Ana wata ga wata: Obasanjo ya kaddamar da yakin zaben Buhari a Amurka

Ana wata ga wata: Obasanjo ya kaddamar da yakin zaben Buhari a Amurka

- Mr Olujonwo Obasanjo, yaron tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo, ya kaddamar da yakin zaben tazarcen shugaban kasa Muhammadu Buhari a kasar Amurka

- Obasanjo, ya ce ya kai ziyara kasar Amurka ne domin neman goyon bayan tazarcen Buhari daga 'yan Nigeria mazauna kasar da kuma mambobin kasashen waje

- Ya bayyana cewa yana goyon bayan tazarcen shugaban kasar ne la'akari da irin kyawawan manufofin Buhari akan bunkasa rayuwar matasa da tsaro na kasar

Mr Olujonwo Obasanjo, yaron tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo, ya kaddamar da yakin zaben tazarcen shugaban kasa Muhammadu Buhari a kasar Amurka.

Obasanjo, wanda shi ne shugaban kungiyar matasa Buhari (BYO), ya ce ya kai ziyara kasar Amurka ne domin neman goyon bayan tazarcen Buhari daga 'yan Nigeria mazauna kasar da kuma mambobin kasashen waje.

Ya bayyana cewa yana goyon bayan tazarcen shugaban kasar ne la'akari da irin kyawawan manufofin Buhari akan bunkasa rayuwar matasa da tsaro na kasar, domin kasar ta zauna lafiya, ta yadda za a samu ci gaba.

KARANTA WANNAN: Babbar magana: Gwamnati za ta haramta shigo da Tumatur dan kasar waje

Ana wata ga wata: Obasanjo ya kaddamar da yakin zaben Buhari a Amurka

Ana wata ga wata: Obasanjo ya kaddamar da yakin zaben Buhari a Amurka
Source: Facebook

Obasanjo ya bayyana hakan a Amurka, inda ya shiga sahun sauran 'yan Nigeria mazauna kasar wajen gudanar da wasu ayyuka da za su haska irin ayyukan da gwamnatin Buhari ta yi a Nigeria.

"Na shiga cikin shirye-shiryen ranar ilimi ta duniya da Majalisar Dinkin Duniya ta ware, wanda sanin kowane ilimi na daga cikin bangarorin da suka samu tagomashi a gwamnatin Buhari.

"Haka zalika na shiga taron tattaunawa kan kasuwanci tsakanin Nigeria da Amurka, inda na hadu da kwararrun 'yan Nigeria da takwarorinsu na kasar Amurka. Na kuma kai ziyara Atlanta domin fadakar da 'yan Nigeria mazauna garin ayyukan Buhari.

Obasanjo ya ce Buhari ne ya bude kofa ga matasa, da zata basu damar damawa da su a cikin harkokin siyasar kasar da kuma tattalin arziki.

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel