Ba bu wani rikici akan kudin yakin zabe - PDP

Ba bu wani rikici akan kudin yakin zabe - PDP

A jiya Litinin babbar jam'iyyar adawa ta PDP, ta musanta zargin samun sabani ko kuma rashin jituwa kan harkokin gudanar da kudade da kuma dukiyar yakin neman zaben kujerar shugaban kasa da ta ke ci gaba da aiwatarwa cikin jihohi 36 da ke fadin kasar nan.

Jam'iyyar ta yi wannan karin haske cikin wata sanarwa da sa hannun babban sakataren ta akan hulda da al'umma, Mista Kola Ologbondiyan, da ya zayyana yayin ganawar sa da manema labarai a jiya Litinin cikin garin Abuja.

Mista Ologbondiyan ya ce wannan zargi maras tushe da rashin madogara ya na da alaka da rashin fahimta gami da kamanceceniya ta abun dariya da ko shakka ba bu 'yan adawa suka kitsa kuma suka ara suka yafa da manufa ta kawo rabuwar kai.

Ba bu wani rikici akan kudin yakin zabe - PDP

Ba bu wani rikici akan kudin yakin zabe - PDP
Source: UGC

Ya ce tsananin adawa ya sanya masu hamayya da jam'iyyar PDP suka kitsa wannan zance sakamakon yadda ta ke ci gaba da samun nasara da goyan baya yayin da mashahurancin dan takarar ta na kujerar shugaban kasa, Atiku Abubakar ya kai wani munzali da ya wuce misali.

Kamar yadda kakakin jam'iyyar ya bayyana, manufa gami hassada ta kawo rikici a jam'iyyar PDP yayin yakin neman zaben ta da 'yan adawa ke ci gaba da kullawa ba bu inda za ta kai su domin kuwa hassada ga mai rabo taki ce.

KARANTA KUMA: Cikin Hotuna: Atiku ya gudanar da taron yakin neman zabe a jihar Zamfara

Babban jigon na jam'iyyar ya ce, adawar masu adawa ba za ta yi tasiri ba kuma karya fure ta ke ba ta 'ya'ya sakamakon yadda tuni aka yi walkiya kuma gaskiya ta bayyana a idanu da zukatan al'ummar Najeriya.

Ya kara da cewa, al'ummar kasar nan tuni suka farga wajen goyon baya na kin karawa sakamakon nagarta gami da hangen kyakkyawar makoma da za su riska muddin Atiku yayi nasara yayin babban zaben kasa da za a gudanar a ranar 16 ga watan Fabrairu.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na zaurukan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel