Ku zabi Buhari domin samun ayyukan yi, inji Farfesa Osinbajo

Ku zabi Buhari domin samun ayyukan yi, inji Farfesa Osinbajo

- Mataimakin shugaban kasa, Yemi Osinbajo ya shawarci matasa su zabi shugaba Buhari da jam'iyyar APC domin su samu nagartatun ayyuka

- Mataimakin shugaban kasar ya ce gwamnatin APC ta cika alkawarin da ta dauka na samar da ayyuka 5,000 ga matasa a karkashin shirin N-Power

- Faresa Osinbajo ya kuma ce gwamnatin tarayya za ta bullo da wani shiri na bawa matasa bashi mai saukin biya domin su kafa sana'o'i

Ku zabi Buhari domin samun ayyukan yi, inji Farfesa Osinbajo

Ku zabi Buhari domin samun ayyukan yi, inji Farfesa Osinbajo
Source: Depositphotos

Mataimakin shugaban kasar Najeriya Farfesa Yemi Osinbajo ya ce Shugaban kasa Muhammadu Buhari zai samar da ayyukan yi masu nagarta ga matasa idan aka zabe shi a karo na biyu.

Osinbajo ya yi wannan furucin ne a karamar hukumar Nsit Atai da ke jihar Akwa Ibom yayin taron yakin neman zabe na jam'iyyar APC da aka gudanar.

DUBA WANNAN: EFCC: Shaida ya bayyana yadda Shekarau da wasu mutane 2 suka kasafta N950m

Ya kara da cewa gwamnati za ta fara bawa matasa bashi mai saukin biya domin su fara sana'o'i inda bankuna za su rika bayar da bashin a karkashin shirin N-Power domin matasan su zama masu dogaro da kansu.

Ya ce tuni gwamnatin ta cika alkawurran da ta yiwa mutane na samar da ayyuka 500,000 ga matasa a karkashin shirin N-Power.

Ya yi kira ga al'umma su zabi jam'iyyar APC da Shugaba Muhammadu Buhari saboda jam'iyyar ne za ta canja rayuwar mutanen jihar zuwa matsayin na gaba wato Next Level.

"Shugaba Muhammadu Buhari ya dukufa domin ganin matasa sun samu ayyuka masu nagarta a kasar nan," inji mataimakin shugban kasa, Osinbajo.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel