Har yanzu ba a daina karkatar da kudaden jama’a a gwamnati na ba - Buhari

Har yanzu ba a daina karkatar da kudaden jama’a a gwamnati na ba - Buhari

- Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayyana cewa har yanzu wasu hukumomi a karkashin gwamnatin sa ba su bar karkatar da kudaden jama’a ba

- Ya kuma yi zargin cewa wasu kuma sun ki su rika zuba hakikanin kudaden shiga da hukumomin ke samu a asusun gwamnati

- Sai dai kuma Shugaban kasar bai ambaci ko da sunan wata hukuma daya da aka kama da laifin ba

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayyana cewa har yanzu wasu hukumomi a karkashin gwamnatin sa ba su bar karkatar da kudaden jama’a ba.

Shugaban kasar ya kuma yi zargin cewa wasu kuma sun ki su rika zuba hakikanin kudaden shiga da hukumomin ke samu a asusun gwamnati.

Buhari ya yi wannan tsokaci ne ranar Litinin, 4 ga watan Fabarairu, a lokacin da ya ke rantsar da hukumar gudanarwar ICPC a fadar Shugaban kasa da ke birnin tarayya, Abuja.

Har yanzu ba a daina karkatar da kudaden jama’a a gwamnati na ba - Buhari

Har yanzu ba a daina karkatar da kudaden jama’a a gwamnati na ba - Buhari
Source: Depositphotos

Sai dai kuma Shugaban kasar bai ambaci ko da sunan wata hukuma daya da aka kama da laifin ba, kuma bai fayyace irin hukuncin da za a yi wa shugabannin hukumomin da ke yin kwangen kudaden ba.

Ya ja kunnen Sabon shugaban hukumar gudanarwar da ya hada kai da bangaren gwamnati, kamar ofishin Akanta Janar domin zakulo hukumomin da ba su zuba kadaden shigar su a asusun gwamnatin tarayya.

KU KARANTA KUMA: Mambobin SDP da PDP 2,000 sun sauya sheka tare da tsohon mataimakin gwamnan Ondo zuwa APC

Bolaji Owasanoye ne aka nada sabon shugaban hukumar gudanarwar ta ICPC.

Owasanoye ya bayyana wa manema labarai cewa ba zai yi kasa-kasa ba wajen ganin an bankado masu wawuran kudaden gwamnati da amfani da kujerun su wajen daka dokan kasa.

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel