INEC na hada kai da APC domin a murde zabe a Jihar Ebonyi – Gwamna Umahi

INEC na hada kai da APC domin a murde zabe a Jihar Ebonyi – Gwamna Umahi

- David Umahi yace INEC na neman hada kai da APC domin murde zaben Ebonyi

- Gwamnan na Jihar Ebonyi yace INEC tana shirin ba APC kyautar kuri’u 200, 000

- Mai girma Gwamnan yace za a yi amfani da PVC na bogi ne domin wannan aiki

INEC na hada kai da APC domin a murde zabe a Jihar Ebonyi – Gwamna Umahi

Umahi yace ana buga PVC na bogi a Arewa domin APC ta murde zabe
Source: UGC

Labari ya kawo gare mu cewa Mai girma gwamna Mista David Umahi na jihar Ebonyi yana zargin hukumar INEC mai zaman kan-ta da cewa tana shirin murde zaben da za ayi kwanan nan domin jam’iyyar APC ta samu kuri’u.

Gwamna Dave Umahi ya bayyana cewa akwai wata makarkashiya da ake kitsawa inda hukumar zabe na kasa watau INEC za ta ba jam’iyyar APC kuri’u har 200, 000 a zaben gwamna da za ayi a farkon wata mai zuwa a jihar sa ta Ebonyi.

KU KARANTA: Kuri'un da Buhari zai samu a 2019 za su fi na 2015 - Umahi ya saduda

Gwamnan ya fadawa Duniya wannan ne a makon nan inda yace ‘dan takarar APC na gwamna a Ebonyi watau Sanata Sunny Ogbuoji ya samu hadin-kan wasu manyan jami’an INEC wanda za ayi amfani da su wajen murde zabe.

Babban gwamnan na jam’iyyar PDP mai adawa yace za ayi amfani da wasu katin zabe ne da wani mai neman kujerar Sanata a jihar a karkashin jam’iyyar APC ya buga wajen kada kuri’un bogi da sunan APC a zaben gwamna da za ayi.

Dave Umahi bai kama sunan Sanatan da ya buga wadannan katin zabe ba, sai dai yace ya fito ne daga wata jihar da ke Arewa maso tsakiya. Gwamnan yayi kira ga mutane su tsare kuri’ar su bayan sun yi zabe domin hana ayi magudi.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel