Zabe: An gano wasu mutane da ke shirin tayar da husuma

Zabe: An gano wasu mutane da ke shirin tayar da husuma

- Rundunar sojin Najeriya ta bayyana cewa ta gano wani makirci da wasu mutane marasa kishin kasa ke kullawa na son kawo hargitsi a zabe

- Tukur Buratai yace sun samu wasu bayanai kan yadda wasu “marasa kisihin kasa” ke kokarin su kawo cikas a wasu sassan kasar a lokacin zaben

- Rundunar ta yi gargadin cewa, za ta ladabtar da duk wani dan kasa ko dan kasashen ketare da ta samu da hannun a yunkurin kawo cikas a zaben

Rundunar sojin Najeriya ta bayyana cewa ta gano wani makirci da wasu mutane marasa kishin kasa ke kullawa na son kawo hargitsi a zaben kasar da za a nan da wasu kwanaki.

Najeriya na shirin gudanar da babban zabenta na yan takarar Shugaban kasa a ranar 16 ga watan nan na Fabrairu.

Shugaban hafsan sojin kasar, Laftanal Janar Tukur Buratai ne ya bayyana cewa sun samu wasu bayanai kan yadda wasu “marasa kisihin kasa” ke kokarin su kawo cikas a wasu sassan kasar a lokacin zaben.

Zabe: An gano wasu mutane da ke shirin tayar da husuma

Zabe: An gano wasu mutane da ke shirin tayar da husuma
Source: Depositphotos

Bayanan a cewar Buratai, sun nuna cewa za a hada kai ne da wasu ‘yan kasar waje wurin ta da husuma a wasu sassan Najeriyar.

Janar Buratai ya bayyana hakan ne yayin bude wani babban taron rundunar sojojin kasa na Najeriya a Abuja a ranar Litinin, 4 ga watan Fabrairu.

KU KARANTA KUMA: Shugaba Buhari ya samu goyon baya daga dan takarar gwamna na APGA a Zamfara

“Bari na fada a daidai wannan lokaci cewa, mun samu bayanai kan yadda wasu kungiyoyi marasa kishin kasa, wadanda ke samun goyon bayan wasu ‘yan kasar waje, kan cewa za su kawo hargitsi a zaben 2019 a wasu sassan kasar nan.” Inji Buratai.

Sai dai rundunar sojin ta Najeriya ta yi gargadin cewa, za ta ladabtar da duk wani dan kasa ko dan kasashen ketare da ta samu da hannun a yunkurin kawo cikas a zaben na Najeriya.

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel