Mambobin SDP da PDP 2,000 sun sauya sheka tare da tsohon mataimakin gwamnan Ondo zuwa APC

Mambobin SDP da PDP 2,000 sun sauya sheka tare da tsohon mataimakin gwamnan Ondo zuwa APC

- Rahoto da ke zuwa mana yayi ikirarin cewa tsohon mataimakain gwamnan jihar Onddo, Lasisi Olugbenga Oluboyo, na a hanyarsa na barin jam’iyyar PDP zuwa APC

- Oluboyo, wanda ya kasance mataimakin gwamnan Olusegun Mimiko, tsohon gwamnan jihar, na ta tattaunawa da shugabancin APC biyo bayan hukuncinsa na son barin jam’iyyar adawa

- Akalla mambobin jam'iyyun adawa 2000 ne suka koma APC

A yan kwanaki da suka rage kafin babban zaben kasar, wani rahoto da ke zuwa mana yayi ikirarin cewa tsohon mataimakain gwamnan jihar Onddo, Lasisi Olugbenga Oluboyo, na a hanyarsa na barin jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) sannan ya yi masauki a All Progressive Congress (APC).

Sahara reporters ta ruwaito cewa Oluboyo, wanda ya kasance mataimakin gwamnan Olusegun Mimiko, tsohon gwamnan jihar, na ta tattaunawa da shugabancin APC biyo bayan hukuncinsa na son barin jam’iyyar adawa.

Mambobin SDP da PDP 2,000 sun sauya sheka tare da tsohon mataimakin gwamnan Ondo zuwa APC

Mambobin SDP da PDP 2,000 sun sauya sheka tare da tsohon mataimakin gwamnan Ondo zuwa APC
Source: Facebook

Legit.ng ta tattaro cewa tsohon kwamishinan noma zai kaddamar da sauya shekarsa a bainar jama’a lokacin ziyarar kamfen din Shugaban kasa Muhammadu Buhari a jihar.

KU KARANTA KUMA: Zabe: An gano wasu mutane da ke shirin tayar da husuma

Shugaban APC na jihar Ondo, Ade Adetimehin ya tabbatar da batun sauya shekaar Oluboye, inda ya bayyana yunkurin a matsayin alamu da ke nuna cewa jam’iyyar ta samu karbuwa a fadin jihar.

A cewar wata majiya ta cikin gida, tace akalla mambobin PDP, SDP, ZLP, da ADP 2,000 ne suka sauya sheka zuwa APC lokacin da Shugaban kasar zai isar da jirgin kamfen dinsa jihar.

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel