EFCC ta maka wasu da ake zargi da saida hannun jarin wani mutumi a kotu

EFCC ta maka wasu da ake zargi da saida hannun jarin wani mutumi a kotu

Mun samu labari daga jaridar Daily Trust cewa hukumar EFCC mai yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa ta cafke wasu mutane da ta ke zargi da laifin karkatar da makudan kudi a Najeriya.

EFCC ta maka wasu da ake zargi da saida hannun jarin wani mutumi a kotu

EFCC ta shiga Kotu da wadanda ake zargi da satar Miliyoyi
Source: Facebook

Kamar yadda mu ka samu labari, hukumar ta EFCC ta gurfanar da Kasumu Ademola, da Salau Mukaila da kuma Ganiu Ishola a jiya Ranar Litinin ne inda ake zargin su da yin awon gaba da wasu makudan kudi da su ka haura Naira miliyan 96.

Hukumar ta EFCC ta gurfanar da wadannan mutane 3 ne tare da wani kamfanin mai suna CSL Stockbrokers, inda ake zargin su da laifuffuka 8. Wadannan laifuffuka sun hada da sata da zamba amince da kuma damfarar Bayin Allah.

EFCC ta mika wadannan mutane ne a gaban babban kotun tarayya na Legas ana zargin su da saida wasu hannun jari na wani mutumi da ya saya a kamfonin Guinness Nigeria Plc, Nestlé Food Plc, Julius Berger Plc, da kuma Unilever Nigeria Plc.

KU KARANTA: Tsohon shugaban Amurka zai gana da Buhari da Atiku a kan zaben 2019

Haka kuma ana tuhumar wadannan mutane 3 da wannan kamfani na CSL Stockbrokers da saida hannun jarin da wannan mutumi Marigayi Joseph Adeyemi ya taba fansa a kamfanin Nigeria Enamelware Plc da kuma Union Bank Plc.

Hannun jarin da wannan mutumi da ya rasu ya mallaka sun kai na Naira miliyan 34. Bayan nan kuma ana zargin wannan mutane 3 da wasu laifuffukan dabam-dabam. Wadanda ake zargi dai sun fadawa kotu a jiya cewa ba su aikata wadannan laifi ba.

Lauyan hukumar EFCC wanda ya shigar da kara watau Nnaemeka Omenwa, ya nemi a cigaba da tsare wadanda ake tuhuma. Yanzu dai Alkali Chukwujekwu Aneke ya daga karar har sai zuwa mako mai zuwa.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel