Allah-kare-bala'i: Munbarin kamfe ya sake ruftawa da 'yan PDP a jihar Ekiti

Allah-kare-bala'i: Munbarin kamfe ya sake ruftawa da 'yan PDP a jihar Ekiti

Wani labari da muke samu yana nuni ne da cewa mumbarin gangamin yakin neman zaben 'yan jam'iyyar adawa ta Peoples Democratic Party (PDP) a daya daga cikin jahohin kudu maso yammacin Najeriya ta Ekiti.

Mun samu dai cewa mumbarin yakin neman zaben ya rufta ne da jiga-jigan jam'iyyar a daidai lokacin da suke magana a gaban dumbin magoya bayan su a wani garin da kawo yanzu bamu tabbatar da ina ne ba.

Allah-kare-bala'i: Munbarin kamfe ya sake ruftawa da 'yan PDP a jihar Ekiti

Allah-kare-bala'i: Munbarin kamfe ya sake ruftawa da 'yan PDP a jihar Ekiti
Source: UGC

KU KARANTA: Wata mata mai ciki ta damfari Dangote

Legit.ng Hausa sai dai ta samu cewa cikin jiga-jigan jam'iyyar ta PDP dake a kan mumbarin lokacin da ya rufta hadda tsohon gwamnan jihar Mista Ayodele Fayose wanda yana ma tsakar magana ne mumbarin ya rufta.

Labarin ruftawar dai ya bazu ne a kafafen sadarwar zamani bayan da wasu daga cikin mahalartar taron gangamin da suka nadi faifan bidiyon suka sake shi a shafukan su.

Sai dai mabanbantan ra'ayoyi sun yi ta dukan junan su musamman ma a kafafen sadarwar zamnin tsakanin masoya da kuma 'yan adawar jam'iyyar ta PDP akan lamarin.

Mai karatu dai zai iya tuna cewa a satin da ya gabata ma dai mumbarin na yakin neman zaben 'yan jam'iyyar ta PDP na dan takarar gwamnan jihar Kebbi ma ya rufta a tsakiyar taro.

Ga dai bidiyon kamfe din nan:

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma legit.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://web.facebook.com/legitnghausa?_rdc=1&_rdr

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel