APC za ta dage wajen ganin an fatattaki Saraki daga Majalisa – Abu Ibrahim

APC za ta dage wajen ganin an fatattaki Saraki daga Majalisa – Abu Ibrahim

- Abu Ibrahim yace APC na kokari wajen ganin Bukola Saraki bai koma Majalisa ba

- Sanatan na APC yace dama babu maganar Saraki ya cigaba da zaman kan kujerar sa

- ‘Dan Majalisar ya bayyana cewa za su yi bakin kokarin sun a ganin Saraki ya sha kasa

APC za ta dage wajen ganin an fatattaki Saraki daga Majalisa – Abu Ibrahim

Sanata Abu Ibrahim yace Saraki zai rasa kujerar sa a Majalisar Dattawa
Source: Facebook

Sanata Abu Ibrahim wanda yake wakiltar mazabar Katsina ta kudu a majalisar dattawan Najeriya a karkashin jam’iyyar APC mai mulki yayi magana game da zaben bana inda yace da wuya Bikola Saraki ya koma kan kujerar sa.

Abu Ibrahim ya bayyana cewa jam’iyyar APC za tayi kokari wajen ganin duk yadda aka yi, Bukola Saraki bai koma kan kujerar sa ba. Ibrahim yace APC za ta hana Saraki lashe zabe a mazabar sa domin hana sa dawowa majalisa.

KU KARANTA: Sanatan APC Andy Uba ya fara hangen kujerar Bukola Saraki

Sanatan na Katsina ya fadawa Daily Trust cewa ko da Saraki ya iya lashe zaben mazabar sa a karkashin jam’iyyar PDP, ba zai sake zama shugaban majalisar dattawan kasar ba. Sanata Abu Ibrahim yace za su dage a kan hakan.

Abu Ibrahim wanda ba zai yi takarar Sanata a APC a zaben 2019 ba, ya bayyana cewa idan har Bukola Saraki ya tsinci kan sa a majalisa bayan zaben da za ayi, ya godewa Allah. Sanatan ya fadawa ‘yan jarida su rubuta su ajiye.

Fitaccen ‘dan majalisar na Katsina yace za su yi bakin kokari su wajen ganin jam’iyyar APC ta tika Bukola Saraki a zaben Sanatan yankin Kwara ta tsakiya wanda za ayi nan da makonni kusan biyu.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel